Ziyarar Merkel a yankin gabas ta tsakiya
April 1, 2007Talla
Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel ta gana da shugaban yankin palasdinawa Mahmoud Abbas a birnin Ramallah.Merkel ta fadawa yan jarida cewa akwai tabbacin cewa zaa sake farfado da tattaunawar samarda zaman lafiya tsakanin palasdinu da Izraela.
Ta bayyana cewa burinsu a nahiyar turai shine a samu zaman lafiya tsakanin wadannan bangarori guda biyu na yankin gabas ta tsakiya,kuma zasu bada dukkan goyon bayansu domin ganin an cimma hakan.
Angela Merkel wadda ke ziyarrata ta farko a wannan yanki a matsayin shugabar kungiyar tarayyar turai ,ta bayyana cewa cimma sasansanta bangarorin biyu,zai taimaka matuka gaya wajen samarwa palasdinu yantacciyar kasa ,kusa da izraela.