Ziyarar Merkel ga sojojin Jamus a Afganistan
March 12, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna shakku ko dakarun ƙungiyar NATO za su iya ficewa daga Afganistan a shekarar 2014 kamar yadda aka tsara. A wata ziyarar ba zata da ta kaiwa sojojin Jamus a sansaninsu dake yankin Mazar-i-Sharif Merkel ta ce ko da yake an samu ci-gaba a ƙoƙarin yin sulhu da 'yan Taliban, amma hakan ba kai matsayin da za a iya janye dakarun ba. Da sanyin safiyar wannan Litinin Mekel ta isa yankin a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, domin gane wa idonta aikin da sojojin Jamus ke yi a Afganistan. Daga nan ta buga wa shugaban Aganistan Hamid karzai waya don yi masa jaje game da aika-aikar da sojan Amirka yayi a kudancin ƙasar.
"Daga nan Mazar-i-Sharif na yi magana da shugaba Karzai inda na sake jaddada masa jaje na game da mummunan aikin da sojan Amirka yayi a ranar Lahadi."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe