Ziyarar ministan harkokin wajan Jamus a Afirka
February 23, 2015Babban kudirin wannan ziyara dai na zaman kara kulla dangantakar da ke akwai tsakanin kasashen uku da kasar Jamus ta fannin hadin kai da zuba jari da sauran damarmaki na cudeni in cudeka. Duk da irin tarin ayyukan da ke gaban Ministan harkokin wajen na Jamus Frank-Walter Steinmeier, ga rikicin Ukraine da gabas ta Tsakiya ga rikicin tattalin arzikin Girka, amma kuma ya samu nasarar kammala ziyarar da ya kai a kasashen uku na Afrika. Babbar kalmarsa a kullum ita ce "Samun kusanci ko alaka da kasashen na Afrika" wannan ya sanya burin ganin tabbatar wannan ziyara da ta kasance ta hudu a wa'adin mulkinsa, da kuma kara bada haske kan sabbin manufofin Jamus kan kasashen Afrika.
"Ya kamata mu kalli Afrika ta sabuwar hanya, kamar yadda wasu Jamusawa ke zato, har yanzu Afrika na zama wani dandali na rikici da tada hankula, tabbas akwai rikici, babu ja a wannan fanni, to sai dai ba dukkanin kasashen ne ke da wannan matsalaba saboda akwai wasu wurare da ake samun ci gaba kuma ake zaune lafiya, nan ne mu ke mai da hankalinmu".
Steinmier na nufin kasa irin Rwanda a matsayin wacce lamura suka hau turbar daidaito duk da irin matsalolin da take fuskanta a fannin siyasa da kuma takun saka tsakaninta da makwobtanta wato Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango. Kasar ta Rwanda ba ta gamsuba da yadda dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya karkashin rundinar MONUSCO ke aikinsu ba, inda Jamus ke bada tallafi na sama da Euro miliyan 100 a kowace shekara. Kamar yadda Ministan harkokin wajen Rwandan Louise Mushikiwabo ta bayyana har yanzu 'yan tawayen Hutu na FDLR na kan iyaka inda suke watsa manufarsu ta nuna kyamar kabilar da ba ta suba, kamata ya yi a kawar da su. A cewar Mushikiwabo akwai bukatar sanya hannun Jamus sosai a yankin ganin cewa a yanzu Faransa da Birtaniya da Beljium suke wurin yanzu haka.
Matasa a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango da Ruwanda da Kenya nada kyakkyawan fata akan kasar ta Jamus a wata kididdiga da aka yi wajen jin ra'ayin matasan da ke zama kashi biyu cikin uku na al'ummar yankin, ta shafin Facebook, da dama cikinsu na fatan ganin Jamus ta yi uwa ta yi makarbiya a harkokin da suka shafi tattalin arzikinsu sannan 'yan siyasa daga kasar ta Jamus su sanya matakan gyara ga 'yan siyasar kasashensu da suka shahara wajen cin hanci da rashawa.