1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar P/M kasar Spain Zapatero a Berlin

April 29, 2004

Sabon P/M kasar Spain Jose Luis Zapatero ya kawo ziyara Berlin inda suka gana da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder. Jamus dai ita ce kasa ta farko da sabon P/M na Spain ya kai wa ziyara a ketare

https://p.dw.com/p/Bvk9
Zapatero da Schröder lokacin ganawarsu a Berlin
Zapatero da Schröder lokacin ganawarsu a BerlinHoto: AP

Bayan ganawar da suka yi da shugaban gwamnati Gerhard Schröder, sabon P/M kasar Spain Jose Luis Zapatero ya fadi cewar akwai wasu muhimman dalilan da suka sanya ya ware Jamus a matsayin kasa ta farko da zai kai mata ziyara. Daya daga cikin dalilan kuwa shi ne muhimmancin da Jamus ke da shi ga kasar Spain. Bugu da kari kuma kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu a yanzu zata shiga wani sabon babi sakamakon canjin gwamnatin da aka samu a fadar mulki ta Madrid, inda ragamar mulkin ta fita daga ‚yan mazan-jiya zuwa ga hannun ‚yan socialist, wadanda manufofinsu na ketare suka banbanta da na magabatansu. Misali dai a yayinda ita tsofuwar gwamnatin kasar ta Spain ta sa kafa tayi fatali da tsarin rabon kuri’a da daftarin mulkin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ya tanada, ita sabuwar gwamnatin a karkashin Jose Luis Zapatero ta bayyana shirinta na cimma daidaituwa akan wata manufa mai sassauci tsakanin dukkan wadanda lamarin ya shafa. Schröder ya yaba da haka matuka ainun inda yake cewar:

  • O-Ton schröder:

    "Ich habe mit....

    Na yi murna da farin cikin jin cewar gwamnatin kasar Spain ba ta da wata matsala a game da tsarin nan da aka kira na tagwayen rinjaye a daftarin mulkin kasashen Turai.

    A sakamakon sabani akan tsarin kuri’ar ne aka kasa cimma daidaituwa wajen wanzar da daftarin tsarin mulkin. Kasashen Spain da Poland sun bayyana adawarsu da tsarin. Amma ga alamu an fara samun canji ga lamarin. Zapatero ya bayyana hakikancewarsa a game da cimma daidaituwa nan da karshen watan yuni mai zuwa. Hadin kan nahiyar Turai shi ne abin da gwamnatinsa zata ba wa fifiko a manufofinta na ketare. Zapatero dai sai ya kara da cewar:

  • O-Ton Zapatero

    "Das heißt....

    Hakan na ma’ana ne cewar Spain ta amince da rawar da kasashen Jamus da Faransa ke takawa bisa manufar hadin kan Turai. A waje na babu wata tsofuwa ko wata sabuwar Turai sai dai wata hadaddiyar nahiya mai al’uma daya.

    A nasa bangaren shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya bayyana ra’ayin yiwuwar gudanar da wani taron kolin da zai hada da dukkan shuagabannin kasashen Spain da Jamus da Faransa a karkashin wannan yanayi. Amma fa hadin kai tsakanin Jamus da Spain ba zai tuke ne kawai akan manufofin hadin kan Turai ba, abu ne da zai hada da manufofin Iraki da MDD. Sabuwar gwamnatin kasar ta Spain tuni ta canza alkibla a manufofinta dangane da Iraki. Jim kadan bayan darewarsa kan karagar mulki P/M Zapatero ya janye sojojin kasar su kimanin 1300 daga Iraki. Ya ce tun da farkon fari yake adawa da farmakin da aka kai wa Iraki ko da yake gwamnatinsa zata ba da gudummawa iya mustada’a domin sake gina kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita.