Ziyarar Paparoma a Mexico
March 24, 2012Shugaban darikar Roman Katolika na duniya, ya fara rangadin kwanaki uku irinsa na farko a kasashen yankin Latine Amurika masu amfani da halshen spananci.
A Mexico dake matsayin matakin farko Paparoma ya samu gagaramin tarbe.
A kan hanyarsa ta zuwa kasar Mexico, dake matsayi ta biyu wajen yawan kiristoci mabiya darikar Roman katolila, Benedikt na 16 ya bayyana wajibcin daina safara miyagun kwayoyi, wanda kasar ta yi fice akai.
Kiddidigar ta nuna cewa, fiye da mutane dubu 50 suka rasa rayuka a shekarun baya-bayan nan, dalili da yake-yake tsakanin manyan diloli kwaya, abinda ya dushe tarmamuwar shugaba Felipe Calderon na Mexico, wanda zai fuskanci saban zaben shugaban kasa a watan Juli na wannan shekara.
Dubunan jama'a ake sa aran za su halarci sallar da Paparoma zai jagoranta gobe idan Alah ya nuna mana.
Bayan Mexiko Benedikt na 16 zai ziyaraci kasar Cuba ranar Litinin mai zuwa inda zai kara karfin gwiwar ga mahunkuntan kasar, suka kara himmantuwa wajen shimfida tafarkin demokradiya da kuma kara samun nutsuwa cikin imani.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala