Ziyarar Paparoma a yankin Gabas ta Tsakiya
September 14, 2012A wannan Juma'ar ne Paparoma Benedikt na 16 ya fara yin wata ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya inda ya fara yada zango a kasar Lebonon. Wannan ziyarar ta kwanaki ukku za ta bashi damar isar da sakon zaman lafiya a kasar Siriya inda ake ci-gaba da gobza fada wanda kuma bisa ga dukkan alamu ke shirin daukar wani sabon salo na rikicin addini. Rahotani daga fadar Vatican sun ce da saukar sa a filin jirgin saman Beyrouth na Lebonon Paparoman dan shekaru 83 zai fara ganawa da hukumomin kasar musamman Michel Sleiman wanda shi ne daya tillo shugabn wata kasar yankin kasashen larabawa wanda ba musulmi ba. Wannan ziyarar ita ce karo na biyu a yankin na gabas ta tsakiya, bayan wani rangandin ya yayi a shekara ta 2009 a kasar Saudiya.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi