1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadin kai tsakanin Jamus da Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 17, 2016

Jamhuriyar Nijar ta sha alwashin bayar da hadin kai wajen magance matsalar kwararar bakin haure daga Afirka zuwa nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/1J93G
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Nijar Mahamadou IssoufouHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Jamhuriyar ta Nijar Mahamadou Issoufou ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar aiki da ya kai Jamus a ranar Jumma'a 17 ga wannan wata na Yuni da muke ciki. Issoufou ya ce za su yi kokarin samo mafita dangane da batun bakin hauren da ke biyowa ta Jamhuriyar ta Nijar a hanyarsu ta shiga Turai.

Ya ce "Shugabar gwamnatin Jamus ta nunar da cewa a duk shekara sama da bakin haure 100.000 ke biyo wa ta Nijar su shigo Turai. Za mu gwada shawo kan matsalar 'yan gudun hijira da ga Libiya. Tarayyar Turai na son shawo kan matsalar Libiya, amma a yanzu Libiya na cikin mawuyacin hali kamar yadda kuka sani. Sai dai za mu ga yadda za mu yi mu rinka hana bakin hauren karasawa Libiya."

A nata jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nunar da cewa Jamus za ta tallafawa Nijar kan batun ilimin yara mata tana mai cewa:

"Nijar na da al'umma mai tarin yawa, mun tattauna kan ilimin 'ya'ya mata. A ganina wannan babbar matsala ce. Haka batun tattalin arziki da ma na daina aurar da yara kanana. Muna son mu taimaka matuka da shirinmu na raya kasa."

Issoufuo ya koka kan matsalar rashin tsaro da kasar ta samu kanta sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram, inda ya nemi tallafin kasashen Turai a kan tsaron, yana mai cewa tsaro ba zai tabbata ba sai da ci-gaba kuma babu ci-gaba in har ba bu tsaro.