1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Shugaban Tunisiya a Amirka

Salissou BoukariMay 21, 2015

Shugaban kasar Amirka Barack Obama zai gana da takwaran aikinsa na Tunisiya Béji Caïd El Sebsi a fadarsa ta White House a wannan Alhamis.

https://p.dw.com/p/1FTmT
Beji Caid El Sebsi
Beji Caid El SebsiHoto: picture-alliance/AA/Landoulsi

Ganawa da shugaban na Tunisiya a fadar ta White House na a matsayin wani mataki da ke nunin cewa shugaban na Amirka na goyon bayan kasar ta Tunisiya mai kimanin mutane miliyan goma sha daya, wadda kuma ta yi nasarar shirya ingantaccen zabe a karshen shekarar ta 2014 da ta gabata.

Shugaban na Tunisiya da ya fara wata ziyara tun daga jiya Laraba a kasar ta Amirka, na fatan samun karin huldar harkokin soja tsakanin kasarsa da ta Amirka wajen yaki da ta'addancin da a halin yanzu ya ke barazana ga kasar ta Tunisiya, inda ya kara da cewa idan har Amirka da sauran manyan kasashe suka taimaka musu, to kasar ta Tunisiya za ta kasance abun koyi a nan gaba.