Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a China
August 30, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a birnin Beijing na kasar China. Agendar Merkel ta tanadi ganawa da firaminista Wen Jiabao da kuma yin tattaki i zuwa cibiyar hada jiragen sama na kanfanin Airbus. Hakazalika tawagar jami'an gwamnati da kuma 'yan kasuwa na Jamus da ke rufa mata baya, za su gudanar da sharwarwarin tsakaninsu da takwarorinsu na China a wani mataki na karfafa dangartakar kasuwanci da ke tsakaninsu. Tarayyar Jamus ce kasar da China ta fi huldar kasuwanci da ita a cikin kasashen da ke da wakilci a EU.
Sai dai kuma baya ga batu na tattalin arziki, shugabar gwamnatin Jamus za ta tattauna da hukumomin China kan wasu batutuwa da suka hada da rikicin siyasar Syriya da batun kare hakkin bil Adama da ma dai 'yancin fadan albarkacin baki a China.
Kafin ta shiga jirgi i zuwa Beijing, Merkel ta gana da takwaran aikinta na Italiya Mario Monti inda ta yaba matakan da kasarsa ke dauka domin rage gibin tattalin arziki da ta ke fama da shi. Merkel ta yi kira ga kasar ta Italiya da ta ci gaba da daukan matakan tsuke bakin aljuhu domin a cimma burin daidaita tattalin arzikin kasashen Turai da aka sa a gaba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu