Ziyarar Talabani a kasar Iran
November 27, 2006Shugaban ƙasar Iraqi Jalalal Talabani a yau zai gana da manyan jamián ƙasar Iran a yayin da ake cigaba da kiraye kiraye ga Washington ta nemi hadin kan Iran wajen samar da zaman lafiya a ƙasar Iraqi domin kaucewa faɗawar ƙasar cikin yaƙin basasa.
Ziyarar na daga cikin matakan diplomasiya na baya bayan da mahukuntan Iraqin ke ɗauka a kokarin shawo kan tarzomar dake ƙara yaɗuwa a ƙasar. A watan Satumban da ya wuce P/M Iraqin Nuri al-Maliki ya ziyarci Tehran inda ya sami tabbacin mahukuntan ƙasar wajen baiwa gwamnatin sa cikakken haɗin kai da goyon baya. Yayin da Iran ke zargin sojin ƙawance da Amurka ke wa jagoranci a Iraqi da haddasa tarzomar dake faruwa a cikin Iraqin, a waje guda kuma Amurkan na dora laifi a kan Tehran da kuma Damascus da rura wutar rikici da tarzoma ta ƙin jinin Amurka tare kashe kashe a tsakanin mabiya ɗariku, lamarin dake kara yin ƙamari tun bayan da aka habarar da gwamnatin Saddam Hussaini a shekarar 2003. Manazarta na ganin cewa Iran za ta yi amfani da ganawa da shugaban ƙasar Iraqi Jalalal Talabani domin nunawa Amurka tasirin da take da shi a Iraqi da kuma ƙasashen yakin baki ɗaya.