100912 Westerwelle Nahost
September 10, 2012Wasu 'yan zanga zanga kenan a karshen mako ke yin kira ga fraiminista Salam Fayyad da ya sama musu isasshen iskar gas.Sun kuma shiga wannan zanga-zanga ne domin nuna rashin amincewa da dogaro da Falisdinu ke yi akan Isra'iIa. To sai dai bisa ga dukkan alamu Westerwelle ya jahilci hakikanin halin da ke wakana a wannan yanki. A don haka ne ma yayin ziyarasa a yankin Falisdinawa ya yi kira ga Fayyad da ya yi kokarin samar da dorewar nasarar da ya samu a manufofinsa . Ya ce hakan na zaman gimshiki kafa kasar Falisdinu.
Rikicin Iran da Isra'ila
Daga ne nan kuma ministan harkokin wajen Jamus ya zarce zuwa Isra'ila inda a yayin ganawarsa da shugabannin kasar ya mai da hankali ga shirin nukiliyar Iran yana mai kashedi game da abin ka iya biyo bayan kin Iran na dakatar da wannan shiri nata.Ya ce:
"Babu wani kari da zan yi game da abin da na fada . Burinmu shine a samu mafita daga wannan rikici ta bin hanyoyin siyasa da diplomasiya. Akwai yiwuwar cimma haka. A saboda haka muke mai hankali muke aiki domin samun mafita. To amma duk da haka kowa na bukatar sanin irin halin da za a fuskanta in har Iran ta ci gaba da yin kunnen kashi."
A dai 'yan makonnin da suka gabata a samu radin-radin da ke nunin da cewa sojojin Isra'ila sun yi damarar kai hari kan tashoshin nukiyar Iran. To sai dai kasashen Turai irinsu Jamus da Faransa da Birtaniya sun nuna rashin amincewa da duk wani mataki na gaban kai da Isarela za ta dauka. Ko da yake ministan tsaron Isra'ila, Ehud Barak ya san da hakan, to amma kuma ya gode wa Westerwelle da wannan ziyara tasa. Ya ce:
" Sanin kowa ne cewa Jamus kasa ce da ke sahun gaba tsakanin kasashen duniya, kasa ce da kuma ke nuna rashin amicewa da shirin nukiliyar Iran take kuma taka rawa wajen ganin ta dakatar da wannan shiri. A hakika mun gamsu da wannan matsayi."
Rarrashi ga Isra'ila
Domin ma kwantar da hankalin Isra'ila da kuma yi wa Iran matsin lamba ne ya sa kasashen Kungiyar Tarayar Turai ke tattauna yiwuwar kakaba wa Iran sabon takunkumin karya tattalin arziki. Wani abu da kuma ya dauki hankali shine jiragen ruwa na yaki da Jamus za ta tura wa Masar . A cikin wani sharhi da ya rubuta a jaridar Haaretz wani dan jarida mai suna Barak Ravid ya bayyanar da burin Isra'ila na ba wa masana'antun makaman Jamus ikon shiga tattaunawa a yankin Gabas ta Tsakiya domin samun makamai kare kanta daga kasashe makwabtanta . To sai da Westerwelle ya ce ba za a shiga tattaunawa kai tsaye tare da Netanyahu akan wannan batu ba.
"Ba zan yi bayani dalla dalla game da wannan batu ba . To amma maganar ita ce gwamnatin Jamus za ta yi la'akari da bukatar ba Isra'ila cikakkar kariya a duk shawarar da za ta tsayar."
Westerwelle ya kau da duk wani rashin fahimta da cewa dangantakar Jamus da Isra'il na nan daran.
Za iya sauraton sautin wannan rahoto daga kasa.
Mawallafi: Torsten Teichman/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala