1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Westerwelle a Gabas Ta Tsakiya

January 6, 2010

A wannan Laraba ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ke fara ziyarar aiki karo na biyu a yankin Gabas ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/LM22
Ministan harkokin wajen Jamus Guido WesterwelleHoto: picture alliance / dpa

Ko da yake batun ƙasashen Yemen da Afghanistan ba ya a jerin batutuwan da zai tattauna, amma kalaman da ya yi dangane da taron ƙasashe duniya kan Afghanistan da ake shirin yi a birnin London, ya sha suka. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya fara sabuwar shekara ne da kalamai masu tsauri. A cikin hirarrakin da aka yi da shi ta kafofin yaɗa labaru yayi ƙoƙarin kawad da shakkun da ake nunawa cewa bai cancanci zama riƙe sabon muƙaminsa ba. Jim kaɗan gabanin a shiga sabuwar shekara Westerwelle ya sha suka saboda barazanar da yayi na ƙauracewa taron na birnin London akan Afghanistan, bisa hujjar cewa idan za a tattauna ne kan ƙara yawan dakarun ƙetare a Afghanistan. To sai dai a wata sabuwar hira Westerwelle ya yi bayanin abin da yake nufi.

"Ba barazanar ƙauracewa taron na yi ba. Na yi kira ne da a ɗauki ƙwararan matakai na siyasa. Na yi imani aikin mu a Afghanistan zai yi nasara ne idan mukamayar da hankali wajen gina ƙasar da inganta halin tsaro musamman rundunar sojinta. Amma abu mafi muhimmanci shi ne taimakawa fararen hula ta hanyar inganta harkokin tattalin arzikinta. Na fi goyon bayan samun masalaha ta siyasa."

Westerwelle na adawa da batun ƙara yawan dakaru ba tare da gabatar da wani ƙwaƙƙwaran shirin sulhu a siyasance ba. A wannan Larabar ce ministan harkokin wajen na Jamus ke fara ziyarar aiki karo na biyu a yankin Gabas Ta Tsakiya wadda za ta kai shi ƙasashen Turkiya, Saudiyya, Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Ba a dai shirya wata ziyara zuwa Yemen ba, to amma halin da ake ciki a ƙasar na daga cikin batutuwan da zai tattauna a wannan rangadi.

Ƙasashen duniya sun ƙara mayar da hankalinsu kan ƙasar ta Yemen sakamakon yunƙurin ta da bam cikin wani jirgin saman fasinjan Amirka da wani ɗan Najeriya yayi a ranar 25 ga watan Disamba, saboda kasancewar ɗan Najeriya yana da alaƙa da ƙungiyar al-Qaida a Yemen. Kakakin jam´iyar adawa ta SPD akan manufofin ƙetare Rolf Mützenich ya nuna fargabar cewa nan ba da daɗewa ba Amirka ka iya kaiwa Yemen hari. Ya ce ɗaukar irin wannan mataki zai mayar da hannu agogo baya.

"Mun san cewa al´umar yankin ba sa ƙaunar ganin dakarun Amirka a wannan yanki. Hakan na saka gwamnatocin yankin cikin hali na tsaka mai wuya. A ɗaya hannun kuma ba na jin daidai ne a kai wani harin soji da nufin yaƙi da ´yan ta´adda waɗanda ´yan sanda da hukumomin leƙen asiri za su fi iya yaƙarsu.

Jami´in na SPD ya bawa ministan harkokin wajen na Jamus shawara da ya taɓo batun inganta tsarin tsaron yankin yayin wannan rangadi.

Mawallafa: Bettina Marx/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal