1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen shari'ar Charles Taylor

February 8, 2011

Ranar 8 ga watan Fabrairu ita ce rana ta ƙarshe a shari'ar da ake wa Charles Taylor, tsohon shugaban Laberiya bisa aikata laifuka a yaƙin basasan ƙasar Saliyo.

https://p.dw.com/p/10Cyx
Charles Taylor a lokacin da yake jiran a fara sauraron shari'arsaHoto: picture-alliance/dpa

Lauyar da ke kare tsohon shugaban ƙasar Laberiya Charles Taylor, ta fice daga kotun da ake shari'arsa a fusace, bayan da alƙalan suka hana mata gabatar da shaidar ƙarshe. Alƙalan sun hana wa lauyoyin gabatar da takardun ƙarshen domin sun tsallaka ranar da ya kamata su kawo. Charles Taylor yana birnin the Hague ne na ƙasar Holland inda ake tuhumarsa da laifuka 11 ciki har da laifin yaƙi da kuma cin zarafin bil Adama, sakamakon yaƙin basasan ƙasar Saliyo da aka yi a shekara ta 1990. Ranar 7 ga watan Afrilu ne dai ranar karshe a wannan shari'ar da ta ɗauki shekaru uku da rabi, to amma lauyar da ke kare Charles Taylor, ta ce ya zama wajibi ta fice daga da ɗakin shari'ar, domin a faɗarta an take 'yancin da Charles Taylor ke da shi na kare kansa a shari'ar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal