1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen ziyara Angeller Merkel a China

May 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bux5

Shugabar gwamnatin Jamus Angeller merkell ta kamala ziyara aikin da ta kai ƙasar China.

Ta kai ziyara ƙarshe a babban birnin kasuwancin ƙasar Shangai, inda ta gana da shugaban limaman cocinan wannan ƙasa Jinn Luxian.

A ganawar da ta yi da Praminista Wen Jiabao, da kuma shugaban kasa Hu Jin tao, Angeller Merkell ta bayyana matsayin Jamus, a dangane da batutuwan da su ka jiɓanci kare haƙƙoƙin Jama´a, da sauran al´ammura da su ka shafi diplomatia da cinikaya…………………………………

Kungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama na dunia, na zargin hukumomin China, da ƙaurin suna wajen gudanar da mulkin kama karya.

Sannan sun tantana a kan rikicin makaman nulkeyar ƙasar Iran

A ɓangaren kasuwancin tawagogin ƙasashen 2, sun cimma daidaito, a kan yarjejeniyar bunƙasa saye da sayarwa tsakanin su.

Angeller Merkell, ta bayyana matuƙar gamsuwa da wannan ziyara farko, da tai kai China, a matsayin ta na shugabar gwamnatin Jamus.