290212 EU-Gipfel
March 1, 2012Tun lokacin da ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro suka shiga matsalar tattalin arziki, kusan ko wane taron da shugabannin ƙasashen ke yi, babu abinda ke mamaye shi, illa batun ceto ƙasashen da suka yi kusan durƙushewa. Sai dai a wannan karon shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, ya yi ƙoƙarin nuna wa yan jarida cewa akwai sakel, inda yace akwai batun Girka taron, amma batun sauye-sauye a kasafin kuɗaɗen ƙasashen Tarayyar Turai shine zai kasance gaba a taron da shugabannin suka buɗe a birnin Brussels.
"Batare da yin ƙarin gishiri ba, ina ganin zamu iya gamsuwa, mun fara ɗaukar ingantattun matakai da za su kai ƙasar Girka gaci. Don haka ina tsammanin wannan taron ƙasashen EU zai banbanta da waɗanɗa suka gabata."
Manufar Taron
A wannan taron shine dai ba'a fayyace tsarin da shugabannin suka shirya faɗa ba, aksarin shugabannin na son sanyya hannu kan matakan ceto tattalin arziki da suke ɗauka a lokacin taron. A kan batun da ya shafi ƙasar Girka dai, kusan shugabannin sun fara fidda wani tsammanin, domin arzikin ƙasar sai ƙara rugujewa yake yi, yan ƙasar da ke adawa da shirin tallafin sai ƙara bazuwa suke a titinu suna bore. Abinda kuma ya ƙara kawo shakka a zukatan shuganiin ƙasashen dake bada tallafi. A jawabinda ya yi gaban majalisar dokin Girka, shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turai Martin Schulz cewa ya yi.
"Abinda ƙasashen EU ke fatan gani shine, wata alama ta haɗin kai, da yanci, haɓakar demokraɗiyya da ci gaba. Tutar Tarayyar Turai buƙatar ta ɗaya ne ga ko wace ƙasa. Don haka an zuba ido bawai ga nan Girka kaɗai ba, harda sauran ƙasashen Tarayyar Turai"
Fiddan tsammani kan Girka
A matsayin sa na dan ƙasar Jamus, shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turai, Schulz yana ganin sannu a hankalin dangantakar ƙasashen Jamus da Girka ta na rugujewa.
"Wannan tattalin arzikin zamani a Turai, yana barin kashi 40 cikin ɗari na matasa a rashin aikin yi. Wannan kuwa ba shine kadai bangaren da ya shafa ba, amma harga tsarin demokradiyya a Turai"
Yanzu haka dai babban ƙalubalen dake kagaban ƙasashen Tarayyar Turai shine su inganta fannin ilimi, zuba jari da samar da makashin da baya gurbata mahalli. Amma batun ceto tattalin arzikin ƙasashen ya kankane duk irin wannan mahimman abubuwa da ake buƙata. Sai dai kwamishinan kuɗi na EU Olli Rehn cewa ya yi
Shigar Sabiya cikin EU
"Mu a hukmar EU muna ganin ya zama dole, mu tabbatar da haɓaka tattalin arzikin ƙasashen dake amfani da Euro, mu shawo kan matsalolin da muke fiskanta, domin sake farfadowa"
Ɗaya daga abinda ke cikin jadawalin taron dai shine, batun shigar da ƙasar Sabiya a ƙungiyar EU, bayan da suka warware batun ƙasar Kosovo, sai dai adawan da Romeniya ta nuna ya kawo cikas. Amma ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerlle cewa ya yi.
"Kosovo da Sabiya sun cika ƙa'idar da muka shinfiɗa. Don haka yana da mahimmanci a matsayinmu don cika alƙawarin da maka yi"
Ana saran shugabannin EU za su taɓo batun ƙasar Siriya inda za su yi ƙira ga MDD ta sauke nauyin dake kanta na kare al'ummar Siriya, kana batun agazawa ƙasashen arewacin Afirka da aka yi juyin-juya hali, shima zai shiga jadawalin.
Mawallafa:Christoph Hasselbach/Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu