Ƙasashen Turai masu amfani da kudin euro na cikin tsaka mai wuya
December 6, 2011A halin da ake ciki hukumar ta baiyana ƙarfin ƙasashe goma sha biyar daga cikin ƙasashe goma sha bakwai masu amfani da kuɗin euro da cewa ya yi rauni matuƙa. Hakan dai na nufin cewa matsayin ƙasashen na iya faɗuwa ƙasa nan da watanni uku masu zuwa. Hukumar ta Standard & Poor's ta ce tattalin arzikin nahiyar turai ya yi rauni sosai a 'yan makonnin nan lamarin da ya jefa ɗaukacin ƙasashen yankin masu amfani da kuɗin euro cikin ruɗani. Hukumar ta ƙara da cewa ƙasashen da ke matsayi na uku a mizanin tattalin arziki kamar Jamus da Netherlands da Finland da Luxemburg da kuma Austria na fuskantar barazanar koma baya zuwa matsayi na biyu yayin da Faransa da sauran ƙasashen kuma su ma suna fuskantar barazanar faɗuwar daraja. Sai dai kuma a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa ƙasashen Faransa da Jamus sun ce za su yi dukkan abin da ya wajaba wajen samar da daidaituwar al'amura a ƙasashen na euro kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nunar " Abin da hukumar sa ido kan ƙarfin ƙasashe na biyan bashi ta yi, abu ne da ke ƙarƙashin huruminta ta yi hakan. Za mu gudanar da taro a ranaikun Alhamis da Juma'a inda za mu yanke shawara akan matakai da muka yi imani masu muhimmanci ne waɗanda za su taimaka wajen sanya ɗa'a da daidaituwar al'amura a ƙasashen masu amfani da kuɗin euro".
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi