1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

070311 Westen Nordafrika Nahost

March 7, 2011

Wajibi ne ƙasashen yammacin duniya su sake lale akan manufofinsu game da ƙasashen Larabawa inda al'uma ke jagorantar wani juyin jaya hali.

https://p.dw.com/p/10Uqz
Boren jama'a ya kifar da gwamnatocin wasu ƙasashen arewacin AfirkaHoto: AP

Guguwar canji dake kaɗawa a ƙasashen arewacin Afirka da na yankin Gabas Ta Tsakiya na bukatar sabon tunani ba kawai na siyasa ba a'a har ma da na tatalin arziki. Saboda haka wajibi ne ƙasashen yamma su sake lale game da manufofinsu game da waɗannan yankuna.

Sauyin da aka samu a ƙasashen Tunisiya da Masar da kuma juyin juya halin da bai kammalu ba a Libiya da boren jama'a a Yemen, Bahrain, Oman da kuma Marokko sun zo wa duniya a ba zata inda suka jefa yanayin siyasar ƙasashen yamma cikin juyayi. Ƙasar Amirka da ƙawayenta na Turai sun kwashe shekaru gwammai suna marawa shugabannin kama karya na Gabas Ta Tsakiya da arewacin Afirka baya. Washington na da sansanonin soji da yawa a yankin Golf yayin da tun shekaru 15 da suka wuce ƙasashen Turai ke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai da ƙasashen arewacin Afirka ƙarƙashin yarjejeniyar Barcelona. Wannan yanki dai na da matuƙan muhimmanci ga ƙasashen yamma, musamman Masar da ke zaman wata gada tsakanin Afirka da Asiya, ta shafe shekaru aru-aru a matsayin ja-gaba, inji Mamdouh Habashi wani mai fafatuka na Masar.

Masar ta kasance jigo a yankin Tekun Bahar Rum

"Amirka kan ta ta san cewa tun ba yau ba Masar ke taka muhimmiyar rawa a wannan yanki, saboda kasancewarta a yankin. Hatta Napoleon Bonaparte wanda ya ci Masar da yaƙi a shekara 1798, ya bayyana ƙasar da cewa muhimmiya ce a duniya."

Ägypten USA Libyen Flugzeugträger Kearsarge im Suezkanal
Jirgin ruwan yaƙin Amirka a mashigin tekun SuezHoto: AP

Ga Amirka Masar na zaman ƙashin bayan manufofinta a yankin Gabas Ta Tsakiya, musamman wanzar da zaman lafiya da Isra'ila, yaƙi da masu tsattsauran ra'ayin Islama da kuma samun shiga mashigin tekun Suez.

A dangane da waɗannan dalilai ne da farko Amirka ta ja da baya ta sa ido ga juyin juya halin a Masar, kuma ta damu game da halin da makomar zaman lafiyar ƙasar.

Kyakkyawan shugabanci shi ne ginshiƙin samun ci gaba

Wanzuwar sahihiyar demokuraɗiyya a arewacin Afirka da Gabas Ta tsakiya ka iya zama kyakkyawar damar yin adalci a hulɗar dangantaku tsakaninsu da ƙasashen yamma. Sonja Hegazy ta cibiyar nazarin manufofin ƙasashen Larabawa a Berlin na ganin wannan sauyin a arewacin Afirka a matsayin kyakkyawar dama maimakon barazana.

"Idan muka dubi burin da ta tarayyar Turai ta sa gaba tun a shekarar 1995 game da yarjejeniyar Barcelona, wato kyautata dangantakar siyasa da tattalin arziki da halastacciyar manufar kwararar baƙi, kare haƙin bil Adama. To amma yarjejeniyar ba ta yi aiki ba saboda rashin wata abokiyar hulɗa. Amma idan aka samu gwamnatocin da al'uma ce ta zaɓa a yankin, za a cimma waɗannan bururrukan."

Hakan zai yiwu ne idan ƙasashen Turai suka bawa ƙasashe ƙawayensu na arewacin Afirka 'yanci daidai wa daida na shiga kasuwanninsu, musamman ma ga kayakin albarkatun noma. To sai dai adawar da manoman ƙasashen EU dake a gaɓar tekun Bahar Rum na kawo babban ciƙas. Idan da gaske ƙasashen Turai suke na ganin demokuraɗiyya da kwanciyar hankali sun wanzua arewacin Afirka, to dole su taimaka wa wannan yankin ya tsaya kan ƙafafunsa a fannin tattalin arziki. Dole ne kuma ƙasashen yamma sun yi karatun mun natsu kan yadda za su tinkari mulkin demokuraɗiyya a ƙasashe masu tasowa, amma ba bin buƙatunsu kaɗai a hulɗarsu da waɗannan ƙasashe ba.

Mawallafa: Bettina Marx / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala