Ƙoƙarin Obasanjo a rikicin Cote d'Ivoire
January 10, 2011Talla
Tuni dai tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bar ƙasar Cote d'Ivoire bayan da ya yi ƙoƙarin shawo kan Shugaba Laurent Gabagbo da ya yi ƙememe ya ƙi sauka daga karagar mulki, da ya sauka a cikin limana. A yayin ganawar da ya yi da ɓangarorin biyu Obasanjo ya nuna buƙatar daukar matakan da suka dace domin warware rikicin siyasar da ya kunno kai bayan zaƙen shugaban ƙasar inda yake cewa:
"A duk sanda matsala ta taso ana buƙatar ɗaukar matakai daban daban ne domin warware ta tare da zaɓar matakin gaskiya mai inganci. Ya zuwa yanzu dai ina kyauata fatan samun mafita daga wannan rikici a cikin ruwan sanyi."
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi