Ƙoƙarin tabbatar da tsaro a Najeriya
May 13, 2014Kimanin kwanaki biyu ke nan da gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirgan Jama'a na tsawon sa'o'i 24 a ƙaramar hukumar Kachia da ke a yankin kudancin Kaduna. Tun bayan ɓarkewar wani munmunar rikicin addini da ya auku a ranar Lahadin da ta gabata ,al'amarin da ya janyo salwantar rayuka da ƙone-ƙonen Coci-coci da Masallatai da gidaje da dama.
Dokar ta ɓacin na kawo cikas ga rayuwar al'umma a garin Kachia
Wannan yanayi dai na dokar ta ɓaci a yankin na kawo damuwa ga al'ummar yankin kamar dai yadda wasu jama'ar ke yin ƙorafi, waɗanda ke kokawa da ƙarancin abinci da zaman ɗar-ɗar da zullumi da kuma ke buƙatar gwamnatin ta hanzarta sassauta dokar don ba su damar zuwa neman abinci da sauran abubuwan na buƙata.
Tuni dai ƙungiyoyin da ke fafatukar ci-gaban al'umma da Shugabannin Siyasa da masu faɗa a ji suka fara mayar da martani wanda suke yin Allah Wadai da lamarin kamar yadda Pastor Yohanna ya bayyana.
''Musulmai da Kiristoci na cikin wani mawuyacin hali sakamakon wannan tashin hankali, akwai buƙatar samun fahimtar juna domin tabbatar da zaman lafiya.''
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da wasu rahotannin da wakilanmu na Abuja da Filato da Niger suka aiko mana a kan dambarwar da ake faman yi ta fafutuka tun bayan da aka sace ' yan matan Chibok.
Mawallafi : Ibrahima Yakubu
Edita : Abdourahamane Hassane