Ƙungiyar ETA a Spain ta koma fagen daga
June 5, 2007Talla
Ƙungiyar yan aware ta ETA, a ƙasar Spain, ta yi shelar komawa fagen daga, tare da dakarun gwamnati.
A watan maris na shekara ta 2006, ɓangarorin 2 ,su ka cimma yarjejeiyar zaman lahia, bayan shekaru 40 na yaƙe-yaƙe, wanda su ka yi sanadiyar murtuwar mutane fiye da 800.
Shugabanin ƙungiyar ETA, na zargin gwamnatin Jose Luis Rodriguez Zapatero, da rashin cikwan alƙawari.
Sannan sun yi wasti da zaɓen yan majalisa, da a ka gudanar a yankin Basque,a watan da ya gabata , wanda su ka ce yana cike da maguɗi.
Shugaban gwamnatin ,ya yi Allah wadai, da wannan mataki, wanda ya saɓawa muradin ƙasar Spain.
Yan awaren ETA, na buƙatar girka ƙasa mai cikkaken yanci, a yankin Basque, matakin da gwamnati ta ce, ba za ta saɓu ba, bindiga a ruwa.