310709 ETA Spanien
July 31, 2009A halin da ake ciki Firaministan Spain Jose Luis Zapatero ya yi kira ga jami´an tsaro da su ƙarfafa yaƙin da suke yi da ´yan ta´adda na ƙungiyar ETA kana kuma su inganta matakan kare kansu.
Har cikin dare an ci-gaba da neman waɗanda suka kai wannan hari. ´Yan sanda sun yi ta binciken motoci ko an ɓoye bama-bamai a cikinsu. Hakazalika hukumomin ƙasar ta Spain sun haƙiƙance cewa ´yan ta´addan ƙungiyar ETA da ake zargi da kai wannan hari sun ɓoya a wannan tsibiri. Wataƙila saboda ´yan sandan sun san cewa waɗanda suka aikata wannan ta´asa ba za su yi saurin ficewa daga tsibirin na Mallorca ya sa aka sake buɗe filin saukar jiragen saman tsibirin a jiya da daddare. Yanzu haka dai zirga-zirgar jiragen sama a filin saukar jirgin saman ta koma kamar yadda aka saba.
A halin da ake ciki wani gidan rediyo a Spain ya sanar da cewa ´yan sanda sun cafke wasu matasa biyu namiji da mace waɗanda suka yi hayan wani gidan ´yan yawon shaƙatawa a tsibirin na Mallorca. Sannan jaridar El Mundo ta rawaito cewa da farko wasu mayaƙan ƙungiyar ETA sun kai wata ziyara a wani caji ofis dake birnin Palmanova da nufin kai masa hari a baya.
An dai tsaurara matakan tsaro a tsibrin musamman kasancewar a yau ƙungiyar ta ETA ke bikin cikarta shekaru 50 da kafuwa, hukumomi ba su fid da yiwuwar kai hare hare a faɗin ƙasar ta Spain ba.
Duk da cewa wannan harin kamar wanda aka kai a yankin Burgos dake arewacin ƙasar ta Spain a ranar Laraba da ta gabata ba wanda ya yi iƙirarin kaiwa amma firaminista Jose Luis Zapatero ya yi amanna cewa ´yan awaren yankin Basque ke da alhakin kai harin da yayi sanadiyar mutuwar ´yan sanda biyu.
Ya ce: "´Yan ta´adda da ke zaman kurkuku na lokaci mai tsawo ka iya zama darasi ga waɗanda suka kai wannan hari. Ba su da maɓoya kuma ba za su iya tserewa ba za a kama su a hukunta su za a jefa su kurkuku har bayan ransu."
A dangane da bikin cikar ETA shekaru 50 da kafuwa tun ba yau ba ma´aikatar cikin gidan Spain ta yi ta gargaɗi game da hare haren da ƙungiyar ka iya kaiwa. To amma ba wanda ya yi tsammanin za ta kai munanan hare haren kurkusa da juna. Hasali ma bayan kame wasu ƙusoshin ƙungiyar a watanin baya-bayan nan fatan kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyar ta ´yan aware ya ƙaru. To amma yanzu murna ta koma ciki domin kamar yadda babban alƙalin Spain ya ce ne wato ETA ka iya kai hari a ko-ina, a lokacin da ta ga dama a a faɗin ƙasar ta Spain.
Mawallafa: Nicolas Buschschlüter/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal