Ƙungiyar EU na fatan samun taimakon Rasha wajen tinkarar rikicin Euro
December 15, 2011Rikicin bashin da ya addabi ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin Euro zai taka muhimmiyar rawa a taron ƙolin yini biyu tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turai da ƙasar Rasha, wanda shugaban Rashar Dimitri Medvedev zai halarta. Majiyoyin dilomasiya sun ce gwamnati a Mosko ta nuna shirinta na ba da gudunmawar Euro miliyan dubu goma ga asusun ceto kuɗin na Euro. Daga cikin muhimman batutuwan da Rasha ke son a tattauna a gun taron shi ne na soke neman bisar shiga ƙasa musamman tsakaninta da ƙasashen tarayyar Turai. Medvedev da shugaban majalisar zartaswar EU Herman Van Rompuy na shirin cimma yarjejeniya kan matakan wucin gadi bisa manufa. Taron ba zai tattauna akan batutuwan da ake takadama kais ba wato kamar halin da ake ciki a Jojiya da Libiya da kuma matakan da gamaiyar ƙasa da ƙasa za ta iya ɗauka kan Siriya a dangane da murƙushe 'yan adawa da gwamnatin ƙasar ke yi.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu