1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Hamas ta yi kira ga Larabawa da musulmi da su kai hari kan kadarorin Amirka a yankin Gabas Ta Tsakiya.

November 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bucq

Bayan halakad da fararen hular Falasdinawa 18 da dakarun igwan Isra’ila suka yi a wani harin da suka kai a garin Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza jiya, ƙungiyar Hamas da wasu rukunan ’yan ta kifen Falasdinawan, abokan burminta, sun yi kira ga larabawa da musulmi da su kai hare-hare kan kadarorin Amirka a yankin Gabas Ta Tsakiya. Ban da dai fararen hulan da suka rasa rayukansu a harin da dakarun Isra’ilan suka kai, rahotanni sun ce wasu mutane 40 kuma sun ji rauni. Isra’ila dai ta amince da kai harin kan fararen hular, amma ta ce kuskure ne. Firamiyan ƙasar bani Yahudun, Ehud Olmert ya bayyana nadamarsa ga asarar rayukan fararen hular da aka yi. Tuni dai ƙungiyar Haɗin Kan Turai da kuma Amirka sunn yi kakkausar suka ga harin tare da kiran ɓangarorin Falasɗinawan da na Isra’ila da su yi taka tsantsan. A yau ne dai ake sa ran kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, zai yi wani taro na musamman don tattauna batun tsanatan tashe-tashen hankullan baya-bayan nan a yankin na Zirin Gaza.