1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar HRW ta zargi al-Shabab da cin zarafin aluma

April 19, 2010

HRW ta ce al-Shabab ta jefa rayuwa jamá a kudancin Somalia cikin uƙuba da azzabtarwa.

https://p.dw.com/p/N0TZ
Tambarin ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Human Rights Watch

Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi al-Shabab ta ƙasar Somalia da sanya jamaá a kudancin ƙasar cikin uƙuba da azzabtarwa da kuma cin zarafi. Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin riƙon ƙwarya a Mogadishu da kuma dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar gamaiyar Afirka bisa harbin kan mai uwa da wabi wanda ya haifar da hasarar rayuka da jikata fararen hula. Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adaman ta ce ko da yake al- Shabab wadda ke da alaƙa da al-Qaída ta kawo zaman lafiya a kudancin Somalia, to amma jamaá na ɗanɗana kuɗarsu musamman mata bisa irin gallazawar da ake musu.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu