1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Tarayya Turai ta sakawa wasu shugabannin ƙasar Iran takunkumi

April 12, 2011

Kimanin wasu mayan ma'aikata guda 32 na ƙassar Iran da ake zargi da take hakin bil adama ƙungiyar ta haramta masu taɓa kuɗaɗen ajiyar da su ke da su a cikin Bankuna

https://p.dw.com/p/10s6x
Mahmoud Ahmadinejad,Hoto: AP

Ƙungiyar Tarayya turai ta sakama wasu mayan ma'aikata guda 32 na ƙasar Iran Takumkumi hana taɓa kuɗaɗen ajiyar su a Bankuna tare kuma da hana masu takardun Visa na yin balaguro , Bayan da aka same su da laifin take hakin bil adama.Mutanen waɗanda galibi suka haɗa da mai'aiktan mashara'anta , a kwai rahoton da ya ambato su da hannu a cikin tursasa wa dakuma azbatarwa da ake yi wa yan' adawa dakuma wakilai na ƙungiyoyi kare hakin bil adama na ƙasar.

Ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar waɗanda suka yanke wannan shawara a Lexumburg inda suke gudanar da wani taro sun ce na gaba ne za su baiyana sunayen mutane da wannan hukumci ya shaffa

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal