Referendum Papandreou
November 2, 2011Kusan mako ɗaya bayan ƙudurin taimakon ƙasar Girka da aka cimma a birnin Brussels, piraministan ƙasar ta Girka Giorgos Paoandreou ya ba da sanarwar neman kaɗa ƙuri'ar raba gardama daga al'umar ƙasar akan manufar taimakon. Wannan matakin dai ya zo a ba zata, ko da yake a haƙiƙa piraministan ƙasar Girkar ba ya da wata mafita ta dabam.
Har yau dai ƙasar Girka na ci gaba da zama ƙayar kifi a wuyan ƙasashen Turai. Ba zat ba tsammani, a ranar litinin da ta wuce piraminista Giorgos Papandreou ya ba da sanarwa a game da neman ƙuri'ar raba gardama daga al'umar ƙasar ta Girka domin tsayar da wata takamaimiyar shawara dangane da sabon kundin taimako na ƙasa da ƙasa da ƙayyade yawan bashinta da misalin kashi hamsin cikin ɗari.
A cikin wannan makon ne dai Papandreou zai nemi ƙuri'ar amanna a majalisar dokoki kana a cikin watan janairu mai zuwa al'umar Girka su kaɗa ƙuri'ar ta raba gardama. Bayan wannan sanarwar da piraministan ya ɗauka, wanda ya mayar da kakkaɓe ƙasar Girka daga matsalar bashi, babbar manufarsa ta siyasa, an shiga wani mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi, musamman a kasuwannin hada-hadar kuɗi da ma shelkwatar gwamnatocin ƙasashen Turai.
Domin kuwa tun da farkon fari al'umar Girka na matuƙar adawa da duk wani mataki na tsumulmular kuɗin da ya wajaba ƙasar ta ɗauka, kuma a yanzu su ne za a danƙa wa alhakin tsayar da shawara a game da matakin taimakon da aka sha faman kai ruwa rana kafin a cimmasa. Ƙin yin na'am da wannan kundin na ma'ana ne cewar ƙasar Girka zata tsunduma cikin fatara nan take , ta fita daga gamayyar takardun kuɗin Euro, sannan su kuma ƙasashen Turai su sake faɗawa cikin wata sabuwar matsala ta kuɗi. Ko da yake wannan ƙuri'ar raba gardama da Papandreou ke shirin aiwatarwa tamkar neman tarar aradu da ka ne gare shi, amma a haƙiƙa baya da zaɓi. Domin kuwa da a ce 'yan hamayya a ƙasar Girkan sun ba da cikakken haɗin guiwa, suka rungumi alhakin da ya rataya wuyansu da hannu biyu-biyu ba tare da nuna son kai ba, to da kuwa wata magana da ƙuri'ar raba gardama ma ba ta taso ba. Amma take-takensu yayi daura da haka, musamman ma ɓangaren 'yan mazan-jiya.
Sabon shugaban jam'iyyar ta 'yan mazan-jiya Antonis Samaras shi ne ke jagorantar matakan adawa da matakan daidaita manufofin kuɗin ƙasar Girka tare da yi wa jama'a alƙawarin sake tattauna kundin taimakon da baya da farin jini tsakanin al'umar Girka in har ya ɗare kan karagar mulki. To sai dai kuma kawo yanzu ƙungiyar tarayyar Turai da babban bankin Turai da ma asusun ba da lamuni na IMF ba su fito fili suka bayyana cewar babu wata dama ta sake tattauna kundin a halin da ake ciki yanzu ba. A yanzu an wayi gari ƙasar Girka na fafutukar kaɗa ƙuri'ar raba gardama, a maimakon wata fafutuka ta cimma wata manufa madaidaiciya ta siyasa.
Mawallafa: Spiros Moskovou/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Usman Shehu Usman