Ɓarna da Ambaliyar Pakistan ta haifar
July 31, 2010Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyar ruwan sama da ta addabi yankin arewa maso yammacin Pakistan ya daɗa ƙaruwa. Alƙaluman baya-bayan da hukumomin na Pakistan suka wallafa sun nunar da cewa mutane sama da 830 sun rigamu gidan gaskiya, yayin da sama da mutane miliyon ɗaya suka rasa matsugunansu.
Jami'an agaji na ci gaba da fiskantar matsaloli saboda lalacewar hanya da rushewar gadoji. Majalisar Ɗinki Duniya ta yi alƙawarin ba da taimakon jin ƙai a wuraren da ambaliyar ta fi tsanani. Ita ma Amirka ta tura jiragen sama masu saukar ungula guda bakwai domin tallafawa aikin ceto. Da akwai yiwuwar ƙara fiskantar ruwan sama kaman da bakin ƙwarya a ƙasar ta pakistan daga yanzu har zuwa kwanaki goma masu zuwa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar