Ɗangote ya shirya magance ƙarancin man fetur a Najeriya
April 17, 2013Hamshaƙin ɗan kasuwan Najeriya Alhaji Aliko Ɗangote, ya sanar da cewa zai gina wani katafaren matatar man fetur na zamani a ƙasar da tafi ko wace fitar da ɗayyen mai a Afirka. Alhaji Aliko Ɗangote ya shaida wa kamfanin dillalcin labarai na Reuters cewa, an daɗe ba a gina wata matatar mai ta zamani a Najeriya ba, don haka ya kammala shirin gina katafaren matatarr mai da zai tace gangar ɗanyen mai na kimanin ganga 400.000 a ko wace rana, kafin nan da ƙarshen shekara ta 2016. Ɗangote yace idan har aka kammala wannan matar da ya ware wa kuɗi har dalar Amirka biliyan takwas don gine ta, to tabbas za ta tallafawa ɗaukacin ƙasashen Afirka kudu da Sahara, bawai ga Najeriya kawai ba. Najeriya dai tana da manyan matatun mai biyu a Fatakol da Warri, kana da ɗaya a birnin Kaduna wanda ke baiwa mutane sama da miliyan 170 mai. Babban ƙalubale a Najeriya shine samun wadataccen mai, duk da cewa itace ƙasa mafi arzikin mai a nahiyar Afirka, kuma ɗaya daga ƙasashen da suka fi sayar da man feutr a duniya. Amma ana matuƙar ƙarancin mai a ƙasar wasu lokuta sai mutane sun kwana a gidajen mai don bin layi
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu
RTR