Ɗankwali ga kowa
Samfurorin kallabi sun danganta da hidimar da ake da ita ko aure ko makoki, ga dai dukkanin harƙar matan Afirka na ɗaura ɗankwalin da ya dace, ga yawancinsu abu ne da ya zama dole na sutura.
Kariya ga iskoki
Ɗankwali iri-iri gangariya a kawunan matan Afirka, akwai sigogi da dama da ake yin amfani da kallabi. Misali a Burkina Faso kallabi na zaman tamkar kariya ga ruwan sama, amma kuma babban tsari ne na iskoki da mugun baki, kuma kowa na yin lale marhabin da kallabin.
Dare da rana
''Ina matuƙar son kallabi bisa kai'' inji Kerubo Winnie wata 'yar ƙasar Kenya'' Na fi ganin ana darajatani idan na ɗaura kallabi, idan ko ba ni da shi a kai ni kan damu'' 'Yar jarida mai kimanin shekaru 21 da haifuwa 'yar Mombasa Winnie a kullum tana sanye da kallabinta a gida ko ofis haka ma wajen aure, kai har ma lokacin barci ta kan saka kallabin domin yakan ƙara daidaita gashin kai.
Shiga ta ɗankwali a musulunce
" Ina saka kallabi domin yana fidda kamata a musulunce.Yana birgeni kullum idan zan fita daga gida na kan ɗaurashi'' a cewar Adisa Sara 'yar Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Adisa mai ɗinki 'yar shekaru 23 ta koyi yadda ake ɗaura kallabi da gauggawa daga mahaifiyarta.
Al'adun Afirka
'' Matan Senegal an sansu saboda ficen da suka yi wajen yin rangwaɗa'' a cewar Aissata Kane. Daura kallabi yakan taimaka sosai ga al'adun Afirka. Musulmace amma ta ce: '' Ɗaura kallabin al'ada ce ta Afirka ba ma kawai ga mata musulmai ba.''
Ko wacce sutura na da nata kallabin
Sunana Ramatu Shu’abu. Ina da shekaru 21 ina zaune a garin Fata a ƙaramar hukumar Gombi da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya a Jihar Adamawa. Sana’ata ɗinki. ''Ina son kallabi saboda ''yana ƙara kyau ga mace, kuma ko wane kaya mutum ya sa idan ba ɗankwali ba zai yi kyau ba, yana ƙara fidda mace sosai. Daurin kallabin da na fi so akwai: Stela Obasanjo da ‘Yar adu’a.
Alamu na ballaga wato girma kenan
Fátima Assimuna mai shekaru 38 da ke zaune a garin Pemba a yankin arewacin Mozambik a gurinsu kallabi na ƙara kyau ga mace.''Na fara koyon ɗaurin kallabi tun ina yarinya zuwa girmana tun ina ƙarama na fara ɗaura kallabi.''
'Yan mata zuwa mata
A birnin Accra cibiyar harkoki; mata da sannu a hankali na ɗaura ɗankwali a cewar Junita Sallah 'yar Ghana. " Ina tsamanin kallabi yana ƙara kyau ga mata ina kallon kaina a matsayin babbar mace idan na ɗaurashi.''Junita 'yar jardida mai shekaru 27 ta ce kallabin ya danganta da hidimomi daban-daban.
Ɗankwali ga ma'aurata
Bongi Khumalo na sayar da kayayyaki a bakin teku a Durban a Afirka ta Kudu, kuma ta ɗaura kallabi abin da ke nuna cewar matar aure ce 'yar ƙabilar Zulu. Ta ce: ''Kallabi na ƙara mani mutunci''. Matar mai shekaru 65 ta ce akwai matan aure da dama a nan Durban waɗanda ba su ɗaura kallabin.
Riga ta matan aure
Nana Ama Akyia Barnieh ta ce kallabi wani abu ne na musammun, da za a iya ɗaurwa ran aure. A cikin al'adun Ghana na mutanen AKAN kallabi wata alama ce, idan mace na son yin aure ko samun 'ya'ya. ''Ina son kallabi sosai saboda yana ƙara karramani da kuma al'adunmu'' .
Abin ƙwarai na kirki
Sunana Azahra Cawurgi , ina garin Asada cikin ƙaramar hukumar Tabelote a jihar Agadez , shekaruna18 da haifuwa , duk lokacin da na ɗaura ɗankwali musammun wanga mai suna Bando ina jin dadi sosai , kuma na fara aza ɗankwali tun ina 'yar shekara 15, ranar sai da a kayi gagarumin buki wajen aza mini ɗankwali , kuma wannan kala ina yin shi ne a lokacin biki ko Sallah.