1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Jamhuriyar Nijar: Zanga-zangar masu dakon mai

Gazali Abdou Tasawa SB
April 16, 2024

Jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye wajen tarwatsa zanga-zanga da matuka tankokin dakon mai na kamfanin dillacin man fetur na SONIDEP suka shirya tare da hana sauke lodin man kamfanin.

https://p.dw.com/p/4er7X
Gidan Mai
Gidan MaiHoto: DW

Takaddamar dai ta taso ne a sakamakon zargin da kamfanin na SONIDEP ke yi wa matuka manyan motocin na sace mai a bisa hanya, a yayin da durobobin su kuma ke zargin shugabannin kamfanin da ha'intarsu da kuma amfani da tsaffin kayan aiki wadanda ke bayar da lissafi na karya wajen sauke lodin man.

Karin Bayani: Jamhuriyar Nijar ta samu ci-gaban rayuwar al'umma

Da sanhin safiyar wannan Talata ne dai jami‘an kwantar da tarzoma suka kai farmaki a kan daruruwan durobobin motocin dakon man fetur wadanda suka kashe kawanaki biyu suna bore a bakin babbar cibiyar ajiyar mai ta kamfanin dillancin mai na kasa SONIDEP da ke a bakin garin birnin Yamai. Bayan da jama'an tsaro suka tarwatsa durobobin tankar sun kama da dama a yayin da wasu daga cikin durobobin suka duri daji.

A tsawon yini biyu dai matuka tankokin dakon man sun hana daruruwan motoci sauke lodin man suna masu zargin kamfanin na SONIDEP ta zarginsu da satar mai. To sai dai kamfanin man na SONIDEP na zargin matuka manyan motocin ne da sace wani kaso na man da ake lodo masu daga matatar mai ta kasa da ke a Damagaram zuwa birnin na Yamai.

Kawo yanzu dai da dama daga cikin daruruwan tankokin man da ke girke a bakin babban cibiyar ajiyar Man fetur din ta kasar Nijar da ke a birnin Yamai sun yi nasarar sauke lodin nasu, a yayin da daga nashi bangare kamfanin na SONIDEP ke ci gaba da isar da man zuwa gidajen mai domin kauce wa yankewarsa a cikin birnin.