Jamhuriyar Nijar ta samu ci-gaban rayuwar al'umma
March 14, 2024Shekaru da dama rahoton shekara-shekara na Hukumar Raya Kasashe ta MDD wato PNUD ko UNDP ya shafe yana bayyana Nijar a matsayin ta karshe ko kusa da ta karshe a fannin ci-gaban yanayin rayuwar dan'Adam a Duniya. Sai dai rahoton 2023-2024 ya bayyana cewa Nijar ta daina zama koma-bayan kasashe, inda ta zo ta 189 kuma ta yi kunnen doki da Chadi amma ta tsere wa kasashe uku ciki har da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Soudan ta Kudu da Somaliya.
Rabuwar kai kan dalilin ci-gaban da Nijar ta samu
Wasu ‘yan Nijar na danganta wannan ci-gaba da kasar ta samu a fannin yanayin rayuwar dan'Adam da abin da suka kira tuballan ci- gaba da gwamnatin Mohamed Bazoum ta dora kafin sojoji su kifar da ita. Soule Oumarou na kungiyar FCR na daga cikin masu wannan ra'ayi. Amma Mahamadou Ismael, wani dan fafutika da ke goyon bayan mulkin sojan Nijar na ganin cewar ci gaban da aka samu abun a yaba ne, amma akwai yiwuwar wani makirci ne da kasashen Yamma ke son shiryawa ga Nijar.
Hukumomin Nijar ba su ce uffan ba tukuna
Kokarin da DW ta yi donjin ta bakin hukumar kididdiga ta kasa kan wannan ci gaba da hukumar UNDP ta ce Nijar ta samu ya ci tura, inda babban daraktan ma'aikatar ya ce kawo yanzu ba za su yi wani tsokaci a kai ba har sai bayan sun yi bitar bayanan da rahoton ya kunsa. Sai dai kasar ta Nijar ta yi kaurin suna wajen zama kutal a duniya a shekarun baya.