1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Alamun samun hanyar tattaunawa

Uwais Abubakar Idris AH
August 14, 2023

An fara ganin wata kafa ta yiwuwar amfani da hanyara sasantawa maimakon amfani da karfin soja a kan rikicin Nijar. Wannan ya biyo bayan amincewa da sojojin suka yi a bude tattaunawar sulhu da kungiyar Ecowas.?

https://p.dw.com/p/4V9PA
Tawagar Mallaman addinin Islamar Najeriya tare da firaministan Nijar Lamine Zeine a Tsakiya
Tawagar Mallaman addinin Islamar Najeriya tare da Firaministan Nijar Lamine Zeine a TsakiyaHoto: Gazali Abdou/DW

Jin labarin amincewar da shugabanin mulkin sojan na Jamhuriyar Nijar suka yi na za su sassanta da kungiyar ta Ecowas ya jefa murna da farin ciki a zukattan mautane da dama a Najeriyar musamman wadanda suka nuna adawa da amfani da kafin soja a kan kasar ta Jamhuriyar Nijar da al’ummarta. Domin kuwa tawagar malamman addinin islamar da suka jagoranci kai ga wannan mataki, sun bude wata kafa ce da aka dade ana jiran samunta a wannan kiki-kaka da ke faruwa tsakanin gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da kungiyar ta Ecowas. Sheik Bala lau shugaban kungiyar Izala ta Jibwis da ya jagoranci tawagar ya ce suna sa ran za a daidaita.

Tawagar mallaman addinin Islamar na kyautata zaton cewar za a samu mafita

Tawagar Mallaman addinin Islamar Najeriya tare da Firaministan Nijar Lamine Zeine a Tsakiya
Tawagar Mallaman addinin Islamar Najeriya tare da Firaministan Nijar Lamine Zeine a TsakiyaHoto: Gazali Abdou/DW

Tawagar da ta nada wakilan da za su gana da shugaban na Najeriya domin isar da wannan albishir da kungiyar ta Ecowas ke nema domin bude kofar tattaunawa a kan wannan batu na Jamuriyar ta Nijar. Bayanai sun nuna cewar matakin da kungiyar Ecowas din ta dauka musamman ma dai Najeriya shi ya harzuka sojojin na Jamhuriyar Nijar da suka kai ga nuna tirjiya. To sai dai ga  Abdul Aziz mai bai wa shugaban na Najeriya shawara a fanin yada labaru ya ce tun farko shugaban kasar ya fi son a yi sulhu. Duk da batun yaki da ake yi har ma da batun samar da rundunar shirin ko ta kwana, ga sanata Ibrahim Lamido ya ce tun farko su suka shimfida batu na bin hanyar lumana a kan wannan lamari. Ko da majalisar dokokin Ecowas a zaman da ta yi a karshen mako a Abuja duk da rarabuwar kawunan da 'yan majalisar suka samu, sun waste a kan tura tawaga don sulhunta lamarin. Ga sauran ‘yan Najeriya irin su Abubakar Muhammad Kantoma na bayyana matsayinsu. A yayin da ake jiran mataki na gaba da kungiyar ta Ecowas za ta dauka bayan gabatar da wannan ci gaba da aka samu, ana cike da fatan cewa an kama hanyar fara tattaunawar sulhu a tsakanin gwamnatin mulkin sojan ta Jamhuriyar Nijar da kungiyar ta Ecowas. Lokaci zai bayyana mataki na gaba da za’a dauka da kaidojojin da za’a gindaya a kan bangarorin biyu, sanin cewa dole sai an ciza sannan a hura kafin cimma matsaya. Babbar ayyar tambaya shi ne cewar ko a kan me ECOWAS din za ta tattauna da sojojin wadanda suka riga suka girka majalisar ministoci tare da ci gaba da nade-nade na mukamai. Tun farko ECOWAS din ta dage kan cewar dole ne sai sojojin sun sake mika mulki ga Bazoum Mohammed.