1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau majalisar dokokin Jamus ke tabbatar da zabar Angela Merkel a matsayin sabuwar shugabar gwamnati

November 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvK2

A yau ne yan majalisar dokokin Jamus zasu kada kuriár amincewa da Angela Merkel shugabar Jamíyar Christian Demokrats a matsayin sabuwar shugabar gwamnatin Jamus. Tun da farko sai da shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya gabatar da sunan Angela Merkel ga majalisar dokokin domin neman amincewar su. A makon da ya gabata, manyan jamíyun kasar CDU da SPD suka kammala amincewa da yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa. A yau ne kuma shugaban gwamnatin mai barin gado Gehard schröder yake ban kwana da wannan mukami inda zai mika ragamar mulki ga sabuwar shugabar gwamnatin Angela Merkel. A yanzu dai Angela Merkel zata kasance mace ta farko shugabar gwamnati a tarihin kasar Jamus.