1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AFCON 2021: Najeriya ta lallasa Masar

Ahmed Salisu
January 11, 2022

'Yan wasan Najeriya sun yi wa takwarorinsa na kasar Masar ci daya mai ban haushi a wasan cin kofin kasashen Afrika da Kamaru ke daukar nauyi.

https://p.dw.com/p/45OyR
Wasan AFCON tsakanin Masar da Najeriya
Hoto: Samuel Shivambu/BackpagePix/picture alliance

A ci gaba da gasar cin kofin kasashen Africa na AFCON da kasar Kamaru ke daukar nauyi, a yau an kece raini a wasan farko tsakanin kasar Aljeriya da ke rike da kambun da kuma kasar Saliyo, sai dai a wasan an tashi canjaras ba tare da kowace kungiya ta jefa kwallo a ragar 'yar uwarta ba.

Najeriya da Masar ne suka buga wasa na biyu, kuma Najeriya ta samu nasarar jefa kwallo guda a ragar kasar ta Masar. Da misalin mintuna 30 da fara wasan ne dai dan wasan Najeriya Kelechi Iheanacho ya jefawa kasarsa kwallo kuma aka yi ta dauki ba dadi har aka tashi daga wasan.