1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AfD za ta shiga majalisar dokokin Jamus

Ahmed Salisu
September 24, 2017

Hasashen farko na zaben Jamus da aka fidda ya nuna cewar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta samu kashi 32.5 cikin 100 yayin da jam'iyyar nan ta AfD mai kyamar baki ta samu shiga majalisa da kashi 13.5 cikin 100

https://p.dw.com/p/2kc1Q
Bundestagswahl 2017 | AfD - Armin-Paul Hampel
Hoto: Reuters/W. Rattay

A karon farko jam'iyyar nan ta AfD da ke kyamar baki ta shiga majalisa inda ta samu kashi 13.5 cikin 100. Ita ma dai jam'iyyar FDP ta samu kashi 10.5 cikin 100. Jam'iyyar nan ta Greens da ke rajin kare muhalli ta samu 9.5 cikin 100. Rahotanni da muka samu daga sassan kasar daban-daban ya nuna cewar mutane da dama sun fita kada kuri'a.  Shi dai wannan zabe wani mataki ne girka gwamnati inda jam'iyyar da ke da ke kan gaba za ta nemi wadda za ta yi da ita don kafa gwamnati.