Sharhin Jaridun Jamus kan Afirka
October 9, 2020Bari mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung, wadda ta rubuta labarinta mai taken: "Masu kifar da mulki a Mali na muradin raba madafan iko a sabuwar gwamnatin kasar." Jaridar ta ci gaba da cewa bayan juyin mulki a Mali, akwai fargabar sojoji za su yi kane-kane a kan madafun ikon kasar. A ranar Lahadi ne dai gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta cimma nasarar 'yanto madugun adawa Soumaïla Cissé da wata Bafaranshiya ma'aikaciyar kungiyar agaji da ake garkuwa da su tun daga 2016, inda gwamnatin kuma ta saki mayakan sakai 180 da ke gidan kurkuku.
Tun a watan Maris ne dai aka sace Cisse a lokacin yakin neman zabe, gabanin zabukan kasar ta Mali. A ranar Litinin din makon nan ne aka nada sabuwar gwamnatin rikon kwarya. Sai dai kamar yadda ake zato, yawancin sababbin wakilan majalisar gudanarwa ciki har da ministan tsaro da na cikin gida jami'an soja ne. Amma fararen hula da dama sun samu mukamai. Kasa da watanni biyu da suka gabata ne dai, sojojin suka cafke shugaban kasa da framinista da ministocin kasar masu yawa da sunan ceto.
Ita kuwa jaridar "Die Tageszeitung" sharhi ta rubuta game da ta'azzarar fada tsakanin gwamnati da masu tsananin kishin addini a kasar Mozambik. Yanzu haka dai yunwa da annobar cutar COVID-19, na ci gaba da gallazawa al'ummar yankin da ake fadan. Ta'azzarar fafutukar mayakan sa kan a yankin arewacin Mozambik mai tazarar kilomita wajen 2,000 daga Maputa babban birnin kasar dai, na barazana ga wannan kasa matalauciya mai yawan al'umma miliyan 30 da ke gefen tekun Indiya. Kama daga annobar COVID-19 da durkushewar harkokin lafiya da take hakkin Dan Adam a bangaren jami'an tsaro zuwa uwa uba yunwa.
Yakin da kungiyar 'yan tawaye mai suna Ansar-al-Sunna ta kaddamar da gundumar Cabo Delgado da ke arewaci. Tun daga shekara ta 2017 dai, yakin ya yi sanadiyyar rayukan mutane sama da 2,500. A yanzu haka dai kungiyar ta hade da ta IS da ke fafutuka a sassa dabam-dabam na duniya. Gundumar ta Cabo Delgado dai, ita ce kan gaba na yawan masu corona a Mozambik. Akwai fargabar yaduwar cutar zuwa sassan kasar saboda yadda mutane ke ci gaba da yin hijira zuwa wasu yankunan da ke fama da hare-hare zuwa wasu birane.
"An koma hukuncin gargajiya wajen yakar annobar fyade". Da haka ne jaridar Die Welt ta bude labarin da ta rubuta dangane da sabuwar dokar hukunta masu fyade ga kanana yara ta hanyar dandaka a Najeriya. Akwai doka makamanciyar wannan a Jamhuriyar Czech. Jaridar ta ce watakila a wannan karon kwalliya za ta biya kuidin sabulu wajen daukar matakin da ya dace na hukunta masu aikata irin wannan danyen aiki. Fyade da kisan gilla da aka yi wa daliba Uwavera Omozuwa mai shekaru 22 a cikin Coci a birnin Benin ya tayar da hankali sosai a ciki da wajen kasar.
Ba a Najeriya kadai ba, har a sauran kasashen Afirka mutane sun harzuka kan wannan cin zarafi da ake wa yara. A shekarar da ta gaba ne dai shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya ayyana dokar ta baci a kan cin zarafi ta hanyar lalata. A wannan kasa ta yankin yammacin Afirka dai ana samun kararraki kimanin 8,500 a duk shekara, sai dai manazarta na ganin cewa yawan wadanda ake yi wa fyaden ya fi haka. An dada tsananta dokar hukunci a kasashe da dama ciki har da Afirka ta Kudu, inda shugaba Cyril Ramaphosa ya kira fyade a matsayin annoba ta biyu bayan COVID-19.