1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
July 24, 2020

Batun shari'ar hambararren shugaban kasar Sudan da matsalar tsaro a Najeriya, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3frJO
Sudan Khartum | Ex-Präsident Umar al-Baschir vor Gericht
Tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir na fuskantar sabuwar shari'aHoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

A wannan mako za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta leka kasar Sudan, inda a ranar Talatar da ta gabata hambararren tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir da wasu mukarrabansa suka gurfana a gaban kotu bisa zarginsu da laifin juyin mulkin shekarar 1989 da ya dora al-Bashir din kan karagar mulki. Jaridar ta ce shari'a ta biyu a kan Al-Bashir. Ta ce tsawon shekaru 30 al-Bashir ya yi yana tafiyar da wata gwamnatin kama karya, har zuwa watan Afrilun 2019 lokacin da wani boren talakawa ya yi awon gaba da gwamnatinsa, aka kuma kafa gwamnatin rikon kwarya tsakanin sojoji da farar hula karkashin jagorancin Abdalla Hamdok. A watan Disamban 2019 an yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a kurkuku bayan an same shi da lafin cin hanci da rashawa da halatta kudin haram. Yanzu dan kama karyar mai shekaru 76 na fuskantar hukuncin kisa, idan aka same shi da laifin aiwatar da juyin mulki a kan halastacciyar gwamnati a ranar 30 ga watan Yunin 1989.

Nigeria Rotes Kreuz
Jami'an agaji cikin hadariHoto: Getty Images/AFP/A. Emmanuel

Har yanzu dai jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ce amma a wannan karo ta leka tarayyar Najeriya ne tana mai cewa, kungiyoyin 'yan bindiga sun addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, amma abin takaici shugabannin siyasa sun kasa yin wani katabus na kawo karshen ta'asar. Jaridar ta ce sojoji da ake turawa yankin domin zakulo 'yan bindigar su ma suna fadawa tarkon maharan. Garkuwa da mutane da neman kudin fansa na daga cikin ayyukan ta'asa da 'yan takifen suka kware a ciki. Jaridar ta kara da cewa a wani abu mai kama da shiga rudu, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi wa 'yan bindigar tayin ba su shanu biyu ga kowace bindiga daya da suka mika wa hukuma. Babu tabbas ko wannan sabon shirin zai yi nasara, kasanacewar a baya masu cinikin makamai ne suka yi farin ciki da wannan tayi domin yin musayar hajarsu da shanu tamkar daga darajarsu ne a fakaice.

Afrika Ruanda Coronavirus Roboter Patienten
Matakan dakile corona a RuwandaHoto: picture-alliance/dpa/C. Ndegeya

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan mako tsokaci ta yi kan annobar corona tana mai cewa: Jamus na yi wa dukkan kasashen Afirka kallon masu babban hadari saboda corona, amma yawan masu cutar a wasu daga cikin kasashen na Afirka ko kadan bai kai na kasashen Turai ba. Jaridar ta bayar da misali da kasar Ruwanda, inda mutane 1655 ne aka tabbatar da suna da corona daga cikinsu kuma kasa da kaso uku cikin 100 ne kadai suka mutu. Wannan adadi na kasa sosai idan aka kwatanta da na Jamus, inda kaso biyar cikin 100 na masu dauke da corona suka mutu, amma duk da haka cibiyar Robert-Koch da ke birnin Berlin ta sanya sunan Ruwanda a jerin kasashe masu hadari saboda annobar. Idan aka kwatanta da kasar Brazil, Afirka gaba daya mai yawan al'umma miliyan dubu daya da dubu 300, na da kashi daya bisa uku ne kadai na yawan masu corona a Brazil. Saboda haka sanya Afirka gaba daya a matsayin mai hadari dangane da annobar corona, ba a yi mata adalci ba kuma zai taimaka bisa manufar magance yaduwar cutar ba.