1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
March 26, 2021

Har yanzu dai rikicin yankin Tigray na kasar Habasha na daukar hankalin jaridun Jamus a sharhuna da labaran da suke bugawa ka nahiyarmu ta Afirka.

https://p.dw.com/p/3rEMu
Äthiopien l Premierminister Ahmed Abiy
Firaminsta Abiy Ahmed na HabashaHoto: Phill Magakoe/AFP

A labarin da ta buga mai taken Habasha ta amsa cewa kasar Iritriya ta shiga yakin yankin Tigray, jaridar Die Tageszeitung ta ce bayan suka da kakkausan lafazi da ke kara yin yawa saboda aikata mummunan laifi a Tigray, Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya dorawa abokan huldarsa na Iritriya wani kaso na laifin yakin na yankin Tigray, sai dai ya ce ba shi ya gayaice su ba. Jaridar ta ce sau da yawa Habahsa ta yi ta musanta cewa dakaru daga makwabciyarta Iritiriya sun kutsa yankin Tigray, inda suka marawa sojojin Habasha baya a fadan da aka gwabza da 'yan gwagwarmayar yankin. Kasancewar sojojin Iritiriya a yankin, ya matukar yi wa 'yan Tigray illa. Firaminista Ahmed dai, na kara shan matsin lamba a wasu yankuna na kasarsa da ke da yawan al'umma miliyan 120 da kuma kabilu dabam-dabam har guda 80.

Aikata kisan kiyashi

An amsa aikata laifin yaki a Tigray a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa, a karshe Firaministan Habasha ya mika wuya ga matsin lambar kasashen duniya. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun gabatar da cikakken rahoto na kisan gilla da aka yi wa fararen hula a Tigray. A karshen watan Fabrairu kungiyar Amnesty International ta gabatar da sakamakon binciken da ta yi a garin Aksum, inda a karshen watan Nuwamban 2020 aka halaka daruruwan fararen hula. Sai dai an zargi sojojin Iritiriya da aikata laifin.

Tansania | Amtseinführung Präsidentin Samia Suluhu Hassan
Sabuwar shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu HassanHoto: AP Photo/picture alliance

Shugabar kasa ba zato ba tsammani, inji jaridar Süddeutsche Zeitung a labarin da ta buga kan Samia Suluhu Hassan sabuwar shugabar kasar Tanzaniya, wadda ta sha rantsuwar kama aiki a ranar Jumma'ar makon da ya gabata bayan mutuwar shugaban kasar John Magafuli a tsakiyar makon jiya. Suluhu Hassan mai shekaru 61 a duniya 'yar asalin tsibirin Zanzibar, ita ce shugaba ta shida a Tanzaniya, za kuma ta karasa wa'adin mulkin Magafuli na shekaru biyar. Ita ce ta farko daga yankin Zanzibar mai rinjayen al'ummar Musulmi da ta rike wannan mukami, abin da ya sa wasu kafafan yada labaran kasar ke cewa za ta fuskanci babban kalubale daga na hannun daman Magafuli da Kiristoci masu ra'ayin kishin kasa. Sai dai wasu na masu ra'ayin cewa, tana da cikakken goyon bayan jam'iyyar da ke jan ragamar mulki sannan ana matukar kaunarta a tsakanin Musulmin kasar. Jaridar ta ce lokaci ne zai nuna, ko za ta bi tsattsaurar alkiblar marigayi Magafuli.

Bai wa mai hakki hakkinsa

A wannan shekarar ake sa rai za a mayar wa Najeriya tagullan kan basaraken nan na Benin da Turawan mulkin mallaka suka yi awon gaba da shi zuwa Turai, yanzu haka kuma yake a gidan adana kayan tarihi na Humboldt da ke Berlin fadar gwamnatin Jamus. Tun wasu shekaru ke nan wani gungun masu fafatuka da ake kira Benin Dialog Group da ya kunshi masana gidajen adana kayan tarihi na Turai da Najeriya, ke kokarin cimma matsaya kan yadda za a kwashe kayayyakin tarihin Afirka musamman na tagulla daga gidajen tarihi na Turai domin mayar wa mammalaka na hakika kayansu.