Dage dokar hana zirga-zirga a Afirka
July 2, 2020An dai samu koma bayan a fanonni da dama musamman ma na tattalin arziki da kasuwanci da kuma ilimi, sakamakon barkewar annobar cutar coronavirus da ta addabi duniya. Zirga-zirgar jiragen sama ma ta samu nakasu, kasancewar an sanya dokar ba shiga ba fita a kasashen da wannan cuta tai musu kaka gida. Sai dai tuni aka fara dage dokar hana shige da ficen a kasashe da dama cikin kuwa har da nahiyar Afirka.
A Najeriya ma dai an dauki irin wannan mataki, sai dai kuma za a fara ne da jigilar fasinjoji a cikin gida, inda jiragen za su fara jigilar a ranar Larabar makon gobe, takwas ga wannan wata na Yuli da muke ciki a Abuja da Lagos. Yayin da kuma za a bude filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal da Owerri da kuma Maiduguri a ranar 11 ga watan na Yuli da muke ciki. Ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter, inda ya ce za a bude sauran filayen jiragen saman kasar domin jigilar fasinja a cikin gida a ranar 15 ga watan na Yuli.
Sirika ya kara da cewa za a sanar da ranar da za a bude filayen jiragen saman domin fara jigilar fasinjoji zuwa ko kuma daga kasashen ketare. Laberiya ce dai kasa ta farko a yammacin Afrika da ta bude filayen jiragen samanta, domin fara jigilar fasinjoji, fannin da shi ne ke kawo mata kaso mafi tsoka na kudin shiga.