1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Cutar coronavirus tana kara yaduwa a Afirka

Ahmed Salisu
January 8, 2021

Kasashen Afirka kamar an sauran sassan duniya na ci gaba da fuskantar kalubale wajen yaki da annobar corona wadda ke ci gaba da lakume rayukan mutane.

https://p.dw.com/p/3nhuV
Coronavirus Südafrika | Klinik mit Covid-19 Station
Hoto: RODGER BOSCH/AFP

A halin yanzu dai wannan annoba ta fi illa ga Afirka ta Kudu wadda ya zuwa yanzu fiye da mutane miliyan guda suka kamu yayin da dubbai suka kwanta dama. Wannan yanayi da aka shiga ya kara ta'azzara ne sakamakon karancin kayan aiki musamman irin wanda ke taimakawa maras lafiya wajen yin numfashi.

Birnin Cape Town da ke da yankuna na marasa galihu da dama na daga cikin wuraren da wannan annoba ta coronavirus ke ci gaba yin mamaya, duba da irin yawan sabbin kamu na cutar da ake samu a kullum. Galibin asibitocin birnin na fuskatar kalubale da dama musamman ma a wuraren da aka kebe domin jinya ga mutanen da coronavirus ta kama. 

Südafrika Corona-Pandemie | Arwyp Medical Centre
Hoto: hafiek Tassiem/REUTERS

Karancin gadaje da sauran kayan aiki da ake amfani da su wajen taimakawa masu wannan cuta wajen yin numfashi na daga cikin irin abubuwan da ke ci wa asibitocin Cape Town din tuwo a kwarya. Likitocin da ke aiki a irin wadannan asibitoci sun ce yanayin na da ban tausayi kuma a mafi yawan lokuta su kan kasance cikin tsaka mai wuya domin kuwa ga marasa lafiya msuamman dattijai amma kuma ba yadda za su yi da su saboda irin halin da suke ciki na rashin kayan aiki.

Wani bu har wa yau da jami'an kiwon lafiyar ke kokawa a kai shi ne karancin wajen da za a ajiya wanda cutar ta yi wa mumamunan kamu domin mafi aksarin asibitocin Cape Town din ba su da wadatattun wuraren da za a ajiye irin wadannan marasa lafiya, kazalika ba kwararrun jami'a da yawa da za su kula da su idan an kawo mutanen asibiti. Wnnan lamari ya sanya mutane da dama na rasa rayukansu, batun da ya sanya hukumomi a kasar kara tsaurara matakai na yaki da cutar inda aka rufe gidajen abinci da wuraren shatakawa gami da haramta sayar da barasa. 

Coronavirus | Südafrika Bierbrauer im Lockdown
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. Engelbrecht

Karin Bayani: Corona: Koma-baya a huldar tattalin arziki tsakanin Jamus da Afirka

Duk da cewar wadannan matakai ba su yi wani tasiri na a zo a gani ba, jami'an kiwon lafiya na cewar an dan samu sauki ta wata fuskar don kuwa yawan wadanda ake kaiwa asibitoci sanadiyyar hadurra na mota da makamantansu ya ragu wanda hakan kuma ya ba da dama ga jami'an su mayar da hankalinsu wajen kula da masu corona. Tuni kuma kwararru musamman kan cutuka masu yaduwa irin su Wolfgang Preiser suka fara ba da shawara ga hukumomi kasar kan yadda za su kara bin matakan shawo kan wannan annoba.

Duk da wannan kalubale da ake fuskanta, Preiser na ganin irin yadda aka wahala a zagaye na farko na cutar zai iya shan banban da wannan zagaye na biyu da ake ciki kasancewar mutane da dama a unguwanni na marasa galihu sun yi cutar don haka garkuwar jikinsu ta rigaya ta shirya wajen tirjewa cutar wanda hakan ke nufin da wuya wanda suka kamu a baya suka kamuwa, sai dai likitoci sun ce wannan fa ba abin dogaro ba ne domin haka su kam sun shirya don fuskantar kalubalen da ka iya kunno kai a kwanaki ko makonnin da ke tafe.