1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Rasha da Ukraine ya shafi Afirka

June 2, 2022

Shugaban kasar Senegal kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Macky Sall zai tattauna da takwaransa na Rasha Vladimir Poutine a birnin Sotchi, kan yakin Ukraine da kuma illar da ke tattare da jigilar hatsi zuwa Afirka.

https://p.dw.com/p/4CDXT
 Tarayyar Afirka | Macky Sall
Shugaban kasar Senegal, kana shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU Macky SallHoto: John Thys/AFP

Shi dai Shugaba Macky Sall na Senegal da kuma ke zaman shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU, na neman hadin kan Rasha wajen fitar da alkama da ke jibge a tashar ruwan Odessa ta Ukraine domin kauce wa matsalar karancin abinci a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya. Wannan na zuwa ne, bayan da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya fara amfani da 'yunwa a matsayin makamin yaki sakamakon jerin takunkumai da kasashen Yamma suka aza masa saboda mamaye Ukraine da ya yi.

Karin Bayani: Matsayin kasashen Afirka a rikicin Rasha da Ukraine

Sai dai kasashen Turai sun fada tare da nanata cewa, ba takunkumansu ba ne ke haifar da tsaiko a kasuwancin a abinci a duniya ba hare-haren Rasha ne. Kimanin tan miliyan 20 na hatsin Ukraine ne ake neman hanyar fitarwa zuwa kasashen waje, saboda matsayar da Rasha ta dauka. Masanin tattalin arziki na kasar Togo kuma daraktan cibiyar Afrocentricity Yves Ekue Amaïzo ya ce balaguru Macky Sall zuwa Rasha ya zo a kan gaba, saboda Afirka za ta bayyana matsayinta a wannan rikicin da bai shafe ta kai tsaye ba amma kuma take fuskantar illolinsa.

Najeriya I Alkama I Tsada
Ana fama da tsadar alkama da kasashen Rasha da Ukraine suka fi samarwa a duniyaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images

Hada-hadar kasuwannin ma'adinai da kasashen Afirka suka dogara a baya wajen samun kudin shiga na tafiyar hawainiya tun bayan fara yakin Ukraine din, lamarin da shugaban kungiyar Tarayyar Afirkan AU Macky Sall ya yi gargadin cewa ka iya jefa kasashen nahiyar cikin mawuyacin hali. Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nemi da a dauki matakin da ya dace, domin tabbatar da kwararar kayyakin bukatun yau da kullum irinsu man fetur da iskar gas tsakanin Ukraine da sauran kasashen duniya.

Karin Bayani:

A cewar Yves Ekue Amaïzo masanin tattalin arziki, Najeriya na daga cikin kasashen da suka fi dandan kudarsu sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa ukraine din. Ba a tsammanin cewa Shugaba Sall zai isa Kyiv babban birnin Ukraine, bayan ganawarsa da Vladimir Putin. Amma dai za a yi tattaunawa ta bidiyo tsakanin Macky Sall da shugaban na Ukraine Volodymyr Zelensky a ranar hudu ga wannan wata na Yuni da muke ciki, a yayin taron kolin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO.