Agajin Jamus ga Pakistan
August 15, 2010Jamus ta ce ta ƙara yawan kuɗin agajinta ga mutanen da matsalar ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar Pakistan daga Euro miliyan biyar da ta sanar tun da farko ya zuwa Euro miliyan 15. Za'a yi amfani da kuɗin agajin ne wajen samar da tsabtataccen ruwan sha, da kayayyakin kula da lafiya da kuma abinci. Ministan kula da harkokin bayar da agaji a Jamus, Dirk Niebel ya bayyana cewar tallafa wa masu fama da matsala a ƙasar Pakistan ita ce babbar hanyar kawar da irin faɗa-a-jin da ƙungiyar Taliban da ma sauran ƙungiyoyi ke da shi akan su.
A halin da ake ciki kuma, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, wanda ya kai ziyara a wuraren da matsalar ambaliyar ruwan ta afku ya bayyana wa al'ummomin cewar ɗaukacin ƙasashen duniya na nuna alhinunsu game da halin ƙasar ta Pakistan ta tsinci kanta a ciki, yana mai alƙawarin cewar, Majalisar Ɗinkin Duniya za ta bayar da duk wani tallafi da ya kamata ga kimanin mutane miliyan 20 ɗin da ambaliyar ta shafa. Ban ya ci gaba da bayanin cewar: " Hakanan kuma ina son gane wa idona yadda lamura ke tafiya da irin hoɓɓasar da za'a ƙara yi, kana da buƙatar al'ummomin ƙasa da ƙasa su hanzarta kawo tallafi ga Pakistan.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Halima Balaraba Abbas