Najeriya: An janye shari'ar Aminu
December 2, 2022Talla
Uwargidan shugaban dai ta sha suka daga bangaren kungiyoyin kare hakkin dan adama da ma sauran jama'a kan sanya wa da ta yi a kamo mata dalibin tare da lakadawa masa duka, saboda tuhumarsa da laifin bata mata suna a shafukan sada zumunta.
Yayin da yake gabatar hukuncin sakin Aminu, alkalin babban kotun Abuja Mai shari'a Yusuf Haliru, ya yi kira ga iyaye da su san ido wajen kula da harkokin 'ya'yansu don gudun aukuwar irin haka a nan gaba.
An dai kame Aminu Muhammad ne a ranar 18 ga watan Nuwanban da ya gabata a jami'ar da yake a karatu, bayan da uwargidan shugaban kasar ta bayar da umurnin nemo mata shi sakamakon sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter makale da hotonta tare da cewa ta ci kudin Talakawa.