Aljeriya: Hanyar kawo karshen rikicin Nijar
August 29, 2023Ministan harkokin wajen Aljeriya Ahmed Attaf wanda ya sanar da wannan mataki ya ce gana da kasashen yammacin Afirka kuma dukkaninsu basu amince da matakin da karfin soji wajen kawo karshen rikicin ba.
Shugabannin hafsoshin sojin kasashen ECOWAS dai sun gana a birnin Accra na kasar Ghana domin tattauna yiwuwar tura sojoji Nijar bayan juyin mulkin da dakaru masu tsaron fadar shugaban kasa suka yi a watan yulin da ya wuce.
Kasar ta Aljeriya ta nanata cewa ba ta goyon bayan amfani da karfin soji inda ta yi nuni da sakamakon da ya biyo bayan matakin NATO a Libya a shekarar 2011 lokacin boren juyin juya hali a kan shugaban kasar Muammar Gaddafi.
Aljeriyar ta ce za ta nemi gudanar da taron majalisar Dinkin Duniya domin maido da doka da oda tare da kare hakkin kowane bangare a rikicin da kuma daukar nauyin taron kan halin da ake ciki a yankin Sahel.