SiyasaAfirka
Daukar matakin diflomasiyya a Nijar
August 23, 2023Talla
A wani rubuto da ya wallafa a ashafinsa na X ko kuma Twitter, ministan harkokin kasashen ketaren na Aljeriya Ahmed Attaf ya nunar da cewa Shugaba Abdelmadjid Tebboune ne ya umurce shi da ya fara ziyara a kasashen Najeriya da Benin da kuma Ghana domin tattauna hanyar diflomasiyya maimakon matakin soja. Aljeriya da ta hada iyakar kimanin kilomita 1000 da Jamhuriyar Nijar dai, na adawa da matakin soja a kan sojojin da suka kifara da gwamnati da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ke son dauka. Shugaba Tebboune na Aljeriya dai, ya bayyana daukar matakin sojan da barazana ta kai tsaye ga kasarsa.