1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta aike manzo i zuwa Nijar

August 24, 2023

Sakatare Janar na ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya Lounès Magramane zai fara ziyara a Jamhuriyar Nijar domin ganawa da bangarori daban-daban na kasar a kokarin warware dambarwar da ta kunno kai bayan juyin mulki.

https://p.dw.com/p/4VXhB
General Abdourahmane Tiani
Hoto: REUTERS

Ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta sanar da cewa manzon na musanman zai isa birnin Yamai a wannan Alhamis (24.08.2023) don ganawa da duk masu ruwa da tsaki kan al'amuran Nijar. Burin kasar dai shi ne shawo kan takaddamar da ake tsakananin sojojin da suka kifar da gwamnati Bazoum da kungiyar ECOWAS cikin ruwan sanyi a maimakon daukar matakin soja da Aljeriya ke adawa da shi.

Karin bayani: ECOWAS ta shirya afka wa sojojin Nijar

Ziyarar jami'in diflomasiyya na Aljeriya a Nijar na zuwa ne kwana guda bayan wata ziyara da ministan harkokin wajen kasar ya yi a wasu kasashe makwabtan Nijar da kuma mambobin ECOWAS da suka hadar da Najeriya da Jamhuriyar Benin da Ghana a kan batun.

Karin bayani: Aljeriya: Warware rikicin Nijar ta diflomasiyya

Aljeriya ta dade tana taka rawa wajen warware rikice-rikicen 'yan tawaye da kuma kiki-kakan siyasa a kasanshen yankin Sahel da kuma yankin Larabawa, kuma masharhanta na ganin za ta iya daidaita dambarwar juyin mulkin Nijar cikin diflomasiyya kamar yadda ake fatan.