1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan Sudan na fuskantar matsalar karancin abinci

Mahmud Yaya Azare MAB
February 23, 2024

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da 95% na al'ummar Sudan ba sa iya samun abinci sau daya a rana. WFP ta ce mutane kimanin miliyan 18 na fuskantar matsalar karancin abinci a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4cnTm
Masu ba da agaji na dafa abinci don rabawa kyauta a Omdurman na Sudan
Masu ba da agaji na dafa abinci don rabawa kyauta a Omdurman na SudanHoto: Mohamed Khidir/Xinhua/picture alliance

Kungiyoyin bayar da agaji sun kwashe tsawon watanni suna gargadin cewa 'yunwa ta afka wa Sudan sakamakon cikas ga ayyukan jin kai da kuma karancin kudade. Watanni 10 da suka gabata ne yakin ya jefa kasar Sudan ga "kusan rugujewa", inda akasarin mutanen kasar ke cikin hali na 'unwa.

 Darektan Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya reshen Sudan Eddie Rowe ya bayyana wa manema labarai a Brussels cewar: "A wannan lokacin, kasa da kashi 5% na 'yan Sudan ne ke iya samun cin abinci sau ɗaya a rana."

Karin bayani:Yakin Sudan ya janyo matsaloli

'Yunwa da yaki ya haifar na sa 'yan Sudan kaurace wa matsugunansu
'Yunwa da yaki ya haifar na sa 'yan Sudan kaurace wa matsugunansuHoto: Reuters

Tun a watan Afrilun da ya gabata ne Sudan ke fama da yaki tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun sa-kai na RSF, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da haifar da abin da MDD ta kira "rikicin gudun hijira mafi girma a duniya."   Mutum miliyan tara sun rasa matsugunansu a cikin Sudan, inda Rowe ya ce "mummunar ta'azzarar rikicin da tashe-tashen hankula da dakatar da girbin amfanin gona da yawaitar gudun hijira na ci gaba da jefa miliyoyin mutane cikin wani bala'i na jin kai."

Daga cikin wadanda suke fuskantar matsalar karancin abinci a Sudan, Rowe ya ce akwai "kusan miliyan biyar da ke gab da fuskantar bala'i"  da ke zama mafi munin matakin gaggawa da WFP ke amfani da shi, na biyu bayan 'yunwa. Cikas na isar da kayan agaji na hana iya tantance girman bala'in na 'yunwa a Sudan. Michael Dunford, daraktan yankin gabashin Afirka na WFP ya ce, "akwai babban batu na samar da bayanai don tabbatar da cewa an cimma matsayar da ake buƙata don ayyana fari ko a'a".

 Karin bayani:Al' amura na dada rikicewa a Sudan

Hukumar Samar da Abinci ta MDD na neman magance karancin abinci a Sudan
Hukumar Samar da Abinci ta MDD na neman magance karancin abinci a SudanHoto: AP

Yayin da WFP ke iya kai kashi 10% na kayan agaji ga masu bukata, "akwai manyan sassan kasar da ba a iya shiga. A cikin watan Disamban 2023 ne, wani kutse da dakarun soji suka sake yi ya sa yaƙin ya kai har zuwa jihar Al Jazira da ke Kudu da Khartoum babban birnin ƙasar Sudan.