Sudan tana tsaka mai wuya
July 25, 2023Dubban daruruwan ‘yan kasar ta Sudan ne dai ke bayyana matukar tashin hankali da suke fuskanta tun bayan barkewar yakin da ke faruwa tsakanin sojojin gwamnati da dakaru masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Mohammad Hamdan Daglo, wato dai yakin da ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu.
Karin Bayani: 'Yan gudun hijira na Sudan a Chadi
Don haka ne ma suke kira ga bangarorin masu jayayya, da su yi la'akari da halin da ‘yan kasar suka shiga su kuma duba yiwuwar dakatar da wannan fada domin samun daidaito a Sudan. A wata zantawar da DW ta yi da Omaima Mekki daga Kosti da ke cikin jihar White Nile, ya bayyana matsalolin da suke fuskanta daga mayakan rundunar RSF, sama da watanni biyu da suka gabata, na sace motoci da kuma sace komai da ke gidaje.
Suleima Ishaq Al Khalifa, ita ce ke jagorantar sashen da ke yaki da cin zarafin mata a a gwamnatin kasar Sduan, ta ce a makon da ya gabata sun matan da aka ci wa zarafi a Kahratoum da sauran wasu yankuna, duk kuma sun dora alhaki ne a kan mayakan tsohon mataimakin shugaban kasar.
Rundunar ko ta kwata ta RSF dai a Sudan ta sha musanta zargin da ake yi wa mayakanta na ci wa mata zarafi da ma sace-sacen da ake cewa suna yi.
Jagoran ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, y ace lallai mutane a Sudan na fama da matsalolin da sai wanda ya gani. Mai Magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Eri Kaneko, ta ce kungiyoyi na fama da matsaloli na samun damar kai agaji a wasu yankunan.
A wani sako da ya watsa ta kafafen watsa labarai a makon jiya, kwamandan rundunar RSF Mohamad Hamdan Dagalo, ya ce a shirye yake da a dawo da zaman lafiya a Sudan. Sai dai kuma kakakin rundunar sojin kasar Sudan, Nabeel Abdallah, ya ce kalaman Hamdan Dagalo sun yi hanun riga da abin da mayakansa ke aikatawa.