1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ambaliya na ci gaba da ta'adi a sassan Najeriya

Aliyu Muhammad Waziri MA
August 13, 2021

Ruwan sama mai yawan gaske ya janyo ambaliya a sassa daban-daban na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa. 

https://p.dw.com/p/3yy5i
Katsina Flut Nigeria
Hoto: DW/Y. Ibrahim

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya janyo ambaliya a kananan hukumomin Jama'are da Kirfi inda mutane biyar suka rasa rayukansu a Jama'are yayin da gonaki da filaye kimanin 1,567 suka salwata. 

A Kirfi ma dai gidaje da dama sun rushe sakamakon ambaliyar wanda zuwa wannan lokaci ma babu wata sahihiyar kididdiga da aka samu ta adadin gidaje da dabbobin da al'ummar Kirfin ta yi asararsu. 

Da ma dai tun farkon wannan damina, masana hasashen yanayi suka gargadi jama'a musamman manoma wadanda wannan ambaliya ta fi tabawa a karamar hukumar Jama'are, inda ta shiga kauyuka har bakwai kasancewar akwai babban Kogi a Jama'aren, an kuma samu asarar ran mutane biyar.

Tote durch Überflutungen in Nigeria Afrika Flash-Galerie
Hoto: dapd

Saboda hasashen daminar bana a Bauchi ya gwada akwai yiwuwar samun ruwan sama mai nauyi da zai haifar da ambaliyar kamar yadda Mr. Aboki Rashad Mai Gari na ma'aikatar aikin gona ta jiha ya bayyana wadda a cewarsa tun kafin saukar daminar suka shawarci jama'a kan yiwuwar hakan.

Hukumar tsaftace muhalli ta jiha tana da rawar da take takawa a irin wannan lokaci wadda ma tun kafin daminar ta kan gudanar da aikin gyara magudanan ruwa a sassan jihar don kiyaye matsalar ambaliyar amma kuma jama'a ba ta cika ba ta goyon baya wajan kiyaye zuba shara a hanyoyin ruwan ba.

Zuwa yanzu haka dai hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA ta tura jami'anta zuwa kananan hukumomin Jama'aren da Kirfi don kididdige asarar da jama'a ta yi don nazarin irin tallafin da za a iya samarwa domin rage wa mutane kuncin da suka shiga.