Ambaliyar ruwa ta haddasa mace-mace masu yawa a kasar Spain
October 30, 2024Akalla mutane 63 sun mutu a wata ambaliyar ruwa da ta haddasa barnar rayuka da dukiyoyi a yankin Kudu maso gabashin Spain. Jami'an agajin gaggawa da kafofin watsa labaran kasar sun bayyana cewar ba a iya shiga ko fita wasu kauyuka saboda datsewar manyan hanyoyi. Dama dai, gwamnan yankin Valencia, Carlos Monzon, ya shaida wa manema labarai cewa an gano gawarwakin da ba a san adadinsu ba, amma bai yi karin haske kan ko su wane ne ba.
Karin bayani: Shekara guda bayan ambaliyar ruwa a Libiya
Ruwan sama kamar da bakin kwarya a kudanci da gabashin Spain ya haifar da ambaliya a kan tituna da birane tun a ranar Talata, lamarin da ya tilasta wa hukumomin shawartar mutane da su zauna a gida da kuma su guje wa tafiye-tafiyen da ba dole ba. Wannan ambaliyar ta zama mafi muni a Spain a cikin shekaru 28 na baya-bayan nan. Amma dai firaministan kasar Pedro Sánchez ya aike da wata rundunar soji da ta kware don gudanar da aiki ceto a yankin Valencia.